Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kare gadon al’adu da martabar masarautu a jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, ya bayyana cewa Radda ya yi wannan furuci ne yayin bikin gargajiya na Hawan Magajiya da aka gudanar a Masarautar Daura.
A jawabinsa, Radda ya bayyana muhimmancin tarihi na Daura a matsayin masarauta mafi tsufa a Nijeriya da kuma muhimmin ɓangare na asalin al’adun ƙasa.
“Labarin Daura labarin Nijeriya ne. Katangar tarihi, bukukuwan al’adu masu armashi, da hikimar mutanenta suna tunatar da mu waye mu. Yayin da muke taruwa don Hawan Magajiya, mu tuna: al’adu su ne ruhin ci gaba,” inji Gwamna.
Gwamna Raɗɗa ya sha alwashin ci gaba da kare gadon al’adu, yana mai cewa: “Za mu kare martabar masarautunmu, za mu inganta al’adunmu, kuma za mu tabbatar da cewa ci gaban da muka samu ya ɗore. Ba za mu ja da baya ba. Za mu ƙara ƙarfi tare.”
