Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Zuwan jakadu 10 bikin hawan sallah a Katsina ya nuna cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu a ƙoƙarin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ke yi na samar da tsaro a jihar.
Babban daraktan yaɗa labarai na gwamna Alhaji Maiwada Ɗanmalam ya faɗi haka lokacin da yake magana da manema labarai bayan da jakadun suka kawowa gwamnan Dikko Raɗɗa barka da sallah a gidan gwamnatin Katsina.
Ya bayyana zuwan su Katsina a lokacin bikin sallah ba wai kawar da fargaba da tsoro a zukatan al’umma ba ne kawai,zai samar da dama ga manyan baƙin su duba yiwuwar zuba hannun jari musamman akan ma’adanai.
Ya ce jakadun sun sami damar fahimtar irin cigaba da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samu kan tsaro da yanzu suna da damar da za su faɗawa duniya Jihar Katsina a shirye ta ke ta yi kasuwanci da kowace ƙasa a duniya.
Ɗanmalam ya ƙara da cewa zuwan waɗannan jakadu ya biyo bayan ziyara da gwamna Dikko Raɗɗa ya kai a waɗannan ƙasashe na jakadun domin haɓaka kasuwanci da neman zuba jari a Katsina.
Ya ce wannan ziyarar aiki da yakai a waɗannan ƙasashe an fara ganin alherin ta, musamman ganin yadda jakadun ƙasashen da ya ziyara duk sun zo jihar.
“Hakan ya nuna shirin gwamnatin Katsina na sake fasalin tattalin arzikin jihar ta hanyar haɗaka da haɗin gwiwa”inji babban daraktan.
