FOMWAN ta karrama masu hidimar gyaran masallatai a Sakkwato

Spread the love

Daga WAKILINMU

Reshen Ƙungiyar Matan Musulmi ta Nijeriya (FOMWAN) da ke Jihar Sakkwato ta shirya wa mambobin da shugabannin kwamitin kula da tsaftar masallatan Jumma’a da walimar cin abinci da karrama shugabannin kwamitin, albarkacin ayyukan da suka riƙa gudanarwa lokacin azumin Ramadan.

Jagoran ƙungiyar a Jihar Sakkwato Farfesa Sadiya Umar OON ita ce ta shirya taron, inda ta bayyana cewa an gudanar da walimar ne domin yin godiya da jinjinar ƙarfafa gwiwa ga masu aikin hidimar tsaftace masallatan Jumma’a, waɗanda ke aikin saboda girman Allah, ba tare da an ba su ko sisi ba.

Farfesa Sadiya ta bayyana cewa a baya sun fuskanci ƙalubalen suka daga wasu mutane da ke ƙorafin bai kamata a ce mata suna zuwa sharar masallaci ba. Har sai da aka samu wani malami da ya wayar wa jama’a kai game da tarihin wata sahabiya mai sharar masallaci, a lokacin Annabi (SAW). Bayan ta rasu sai da Annabi (SAW) ya sake yi mata Sallah.

Sannan ta ƙara bayyana cewa, a baya kafin fara wannan aikin shara akasarin masallatan suna kasancewa cikin yanayin ƙazanta da rashin gyara, amma yanzu hakan ya zama tarihi.

A nata jawabin Ameera ta FOMWAN a Jihar Sakkwato Hajiya Zahra’u Maishanu da wasu iyayen ƙungiyar sun bayyana jin daɗinsu da yabawa ga ýan kwamitin sharar masallatan, tare da alƙawarin cigaba da ba da goyon bayan ga ayyukan da suke yi.

A yayin taron an ci an sha an kuma raba kyaututtuka ga wasu da suka yi hidimar aikin sharar masallatan.

By ukarofi