Kwankwasiyya Sahlaniyya ta shirya bikin sallah a Jos

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Masu ruwa da tsaki a siyasar Kwankwasiyya, magoya bayan Jam’iyyar NNPP, da masoya ɗan takarar Sanata a shiyyar Filato ta Arewa, Alhaji Shafi’u Yakubu Sahlan sun yi taron barka da Sallah, don ƙara ƙarfafa zumunci da tattauna batutuwan da suka shafi cigaban siyasar Kwankwasiyya a Jihar Filato baki ɗaya.

Honorabul Shafi’u Sahlan jagoran Kwankwasiyya Sahlaniyya shi ne ya shirya taron da aka yi wa taken, ‘Tsintsiya Maɗaurinki Ɗaya,’ a harabar gidansa da ke cikin garin Jos, inda ya bayyana cewa, manufar taron shi ne a haɗo kan magoya bayan jam’iyyar NNPP da Kwankwasiyya baki ɗaya, don a ƙara tunatar da su nauyin da ke kansu na cigaba da gudanar da ayyukan raya jam’ iyya da kuma ƙara tallata ta wajen jama’a.

Duk da kasancewar, ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, Hon. Shafi’u Sahlan shi ne ya zo na biyu a zaɓen 2024 da aka gudanar, da kotun ƙoli ta tabbatar wa da ɗan takarar Jam’iyyar ADP a matsayin wanda ya yi nasara, duk da zargin tafka maguɗi da ake yi. Amma kwarjini da farinjinin Hon. Shafi’u na cigaba da ƙaruwa a zukatan jama’a masoya da sauran jama’ar gari.

Don haka, yayin wannan taro, an ga dafifin jama’a da suka halarci taron barka da Sallar har da wakilan jam’iyyar NNPP daga ƙananan hukumomi shida na shiyyar Filato ta Arewa, da suka haɗa da Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Jos ta Gabas, Bassa, Barikin Ladi da Riyom.

A jawabinsa, Hon. Shafi’u Yakubu Sahlan, ya ƙara ƙarfafa gwiwar magoya bayansa da ýaýan jam’iyyar NNPP, kada su karaya su cigaba da aikin yaɗa manufofin madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na bunƙasa ilimi da cigaban rayuwar ýan Nijeriya.

Ya yi alƙawarin cigaba da gudanar da ayyukan tallafi da yake bai wa al’umma a ɓangaren ilimi, kiwon lafiya da sana’o’i, tare da tallafawa cigaban jam’iyyar NNPP da rayuwar ýan Kwankwasiyya a jihar Filato baki ɗaya. Ya kuma ƙara da cewa, nan ba da jimawa ba, za a samar da sabbin tsare-tsare da za su ƙara farfaɗo da ayyukan jam’iyyar a jihar.

Wasu da suka yi jawabi a taron da suka haɗa da Mataimakin Shugaban NNPP na shiyyar Filato ta Arewa, Alhaji Hussaini Ya’u, Hajiya Ummuhani Hassan, Hajiya Aisha Yakubu Adam, da shugabar mata Hajiya Jamila Labaran, da shugaban matasan NNPP na Jihar Filato, Hon. Salim Sudais, duk sun ƙarfafa buƙatar magoya bayan Kwankwasiyya su ƙara jajircewa wajen ganin Jam’iyyar NNPP ta cigaba da samun nasara a Filato baki ɗaya.

Sun kuma kira dukkan waɗanda suka yi takara a baya a ƙarƙashin jam’iyyar su fito su mara wa gwagwarmayar da Hon. Shafi’u Sahlan yake yi, don farfaɗo da kima da martabar jam’iyyar a Jihar Filato baki ɗaya.

By ukarofi