Yaƙin kasuwanci tsakanin Chana da Amurka: Wa zai fara zubar da makamansa?

Spread the love

Kamar yadda ake gani, a ‘yan lokutan nan ne wani gawurtaccen yaƙin kasuwanci ya turnuƙe tsakanin ƙasar Amurka da kuma ƙasar Chana, inda kowanne daga cikinsu ke jifar ƙan uwansa da makaman haraji.

Wannan lamari dai wasa-wasa na neman zama babba, kamar yadda jama’a da dama da ke tofa albarkacin bakinsu ke ganin abin a farko kamar ƙaramar magana, saidai a yanzu ta zama babba.

Duk da cewa, Shugaba Trump bai bar kowa ba a harkar haraji da shirye-shiryensa na ‘Make America Great Again’, amma za a iya fahimta ƙarara cewa, akwai lauje cikin naɗi a irin farmakin da yake kai wa Chana ta fuskar kasuwanci. 

Wannan ne ya sa, motsi kaɗan za ka ji wani ƙarin haraji da ya lafta wa ƙasar, ita kuwa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin mayar da martani a inda ya dace.

Ko a baya-bayan nan, Shugaba Donald Trump ya dakatar da harajin da ya lafta wa ƙasashen duniya na tsayin kwanaki 90, saidai a lokaci ɗaya ya ƙara wa Chana da kashi 125%.

Shugaban ya ba da sanarwar dakatar da tsagaita buɗe wuta na tsawon watanni uku kan duk wasu ƙarin harajin da aka ɗorawa masu kai kaya da suka fara aiki da tsakar dare, amma fa ban da Chana.

Trump ya sanar da sabon ƙudurin nasa ne kan shafinsa da je kafar The Truth sa’o’i bayan da kayayyaki daga ƙasashe kusan 90 suka shiga tsaka mai wuya, abin da ake kira harajin harajin da Amurka ta sanya.

Shugaban na Amurka ya kuma bayyana a shafin nasa na sada zumunta cewa, ya ƙara harajin da aka sanyawa kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasar Sin zuwa kashi 125 cikin 100 “inda zai fara aiki a nan take” saboda “rashin girmamawa da ƙasar Sin ta nuna wa kasuwannin duniya.”

A ɓangaren Shugaban Chana Xi Jinping ko kaɗan bai nuna alamun gajiyawa ba a yaƙin kasuwanci da suke gwabzawa da Amurka ba, maimakon haka, cikin azama ya mayar da martani, a ƙoƙarin ganin ya bayyana cewa, yanzu aka fara, ta hanyar mayar da martani da irin makamin da Amurka ke amfani da shi.

Ga dukkan alama dai yaƙin kasuwanci da ke guda tsakanin Amurka da Chana ba shi da alamun sassautawa, domin jim kaɗan bayan ƙarin harajin da Amurka ta sanar na kaso 125%, Beijing ta ci alwashin mayar da martani, wanda hakan ya biyo bayan ƙudurin Shugaban Amurka Donald Trump na sake lafta wa ƙasar ƙarin haraji.

Kafin wannan Trump ya ayyana harajin kashi 104% kan Chana, lamarin da zai sa kayayyakin Chana da ake shigarwa Amurka su dinga biyan kashi 104 idan aka haɗa da na baya da Trump ɗin ya sanar.

Wayoyin hannu, da sinadaran haɗa batiri, da kayan wasan yara, da na’urorin game, su ne mafi yawan kayan da Chana ke shigarwa Amurka. Duk da cewa akwai wasu ababe da dama bayan su.

Chana ba ta yo ƙasa a gwiwa ba, ta sanar da ƙarin harajin kan kayayyakin Amurka da kashi 84.

ƙasar ta ƙara yawan haraji kan kayayyakin Amurka daga kashi 34, zuwa kashi 84 cikin 100, a matsayin martani kan sabon harajin kashi 104, da shugaba Trump ya laftawa kayayyakin ƙasar ta Sin wanda ya gudana a ranar Larabar da ta gabata.

A jiya Alhamis 10 ga watan Afrilun da muke ciki ne sabon harajin na Chana ya fara aiki kan Amurka.

Ga dukkan alamu shuwagabannin biyu ba sa ji kuma ba sa gani kan lamarin, kuma sun yi shirin ba gudu ba ja da baya, domin ko a ranar Laraba sakataren baitulmalin Amurka Scott Bessent ya gargaɗi ƙasashe kan kada su kuskura su goyi bayan Chana, domin a cewarsa yin hakan tamkar sun daɓa wa kansu wuƙa ne.

Tuni dai kasuwannin duniya kama daga na hannayen jari da man fetur musamman a Turai da Asiya suka durƙushe sakamakon hasarar maƙudan kuɗaɗen da suke ci gaba da tafkawa saboda tasirin matakin Trump na tsananta harajin da ya ce ya shafi kowacce ƙasa.

Saidai wannan barazana ko kusa ba ta yi tasiri ga Tarayyar Turai, wato EU ba, inda ta ce dukkanin mambobin ƙungiyar sun amince su maida wa Amurka martanin lafta mata harajin da zai fara aiki daga ranar 15 ga watan nan, wato ranar Talata mai zuwa, kodayake ƙungiyar ta EU ta ce a shirye take ta fasa aiwatar da matakin, idan Amurka ta amince da tayinta na ƙulla sabuwar yarjejeniyar kasuwancin da za ta yi wa kowane ɓangare adalci.

A nata ɓangaren duk da cewa harajin da Donald Trump ya narka wa ƙasashe bai shafe ta ba, Rasha ta bayyana matakin a matsayin ƙasƙantar da dokokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.

Da wannan ne muka kai ga tambayarmu ta wa zai fara ajiye makaman yaƙi tsakanin Chana da Amurka? Duba da cewa, ƙasashe da dama sun fusata da dokokin Shugaba Trump kan harajin, wanda ya shafi ƙasashe masu yawa, wasu na ganin Amurka ce ya fi cancanta ta ajiye makaman yaƙi, domin harin zai yi mata yawa, wato daga sassa da dama za ta samu ire-iren martanin Chana. 

Yayin da wasu ke ganin ko kusa Amurka bai cancance ta fara rusunawa ba, kasancewar tana da ƙarfin da zata iya haɗiye duk wani martani da wasu ƙasashe za su kai mata. Da wannan ne suke ganin Chana ce a ƙasa, don haka ita ce ya fi cancanta ta fara russunawa, in ya so ita Amurka ta bada kai bori ya hau.

Da wannan ne za mu kai duba kan wasu bayyanai da wasu masana suka yi kan lamarin.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, wani babban mai bincike a sashen Chana Center na cibiyar The Conference Board, mai suna Afredo Montufar-Helu, ya ce, “Kuskure ne a yi tunanin Chana za ta bayar da kai ta cire harajin da ta saka ita kaɗai. 

“Ba wai kawai zai sa Chana ta zama raguwa ba, zai jawo Amurka ta ƙara neman wasu buƙatun. Yanzu mun kai wata gaɓa da za ta iya sakawa a daɗe cikin rikicin.”

Da wannan za mu iya cewa, mai karatu, nuni ya ishe mai hankali. Idan ka karanta, sai ka zama alƙalin lamarin.

By ukarofi