Kisan Uromi: Gwamnatocin Tarayya da Edo sun kafa kwamitin bincike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis ne Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya ce Gwamantin Tarayya da haɗin-gwiwar ta Edo sun kafa kwamitin bincike game da kisan mafarauta a Uromi da ke jihar.

Okpebholo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar kwamitin bincike daga Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo a Gidan Gwamnatin jihar dake Benin.

Ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhininsa game da lamarin, wanda hakan ya sa ya ke ƙoƙarin tabbatar da samar da aminci ga walwalar al’umma yayin da ake ƙoƙarin yin adalci game da kisan.

Ya kuma ce, lamarin ya yi sanadin yin hoɓɓasa da gwamnatinsa ta yi wajen ganin sun samar da hanyoyin tabbatuwar ɗorewar zaman lafiyar al’umma.

Haka kuma Okpebholo ya ce, su mutane ne masu son zaman lafiya da waɗanda ke zama a jihar da ba ƴaƴanta ba, ya na mai bada misali da tarayyar su da mutanen Kano ta fuskar kasuwanci.

A nasa jawabin, Kwamared Abdulsalam Gwarzo ya yaba wa Okpebholo bisa ziyarar da ya kai Kano a lokacin da abin ya faru.

Ya ce, sun je Edo ne don nuna godiyarsu ga gwamnan ganin yadda musamman ya je Kano don nuna kaɗuwarsa game da iftila’in.

Haka kuma, Gwamna Okpebholo da tawagar sun ziyarci Uromi, inda suka gana da al’ummar Hausawa da ke yankin.

By Babaji