Kotu ta yi watsi da ƙarar neman ƴancin ɗan-adam da Nnamdi Kanu ke yi kan Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Alƙali Iyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya, ya yi watsi da ƙarar Naira biliyan 50 da Shugaban ƴan ƙungiyar fafutukar kafa yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya shigar akan Gwamantin Tarayya.

Alƙalin a yayin sauraron ƙarar, kasancewar ba a samu wakilci daga Kanu ko gwamnatin Tarayya ba gami da rashin cike ƙa’idodin karɓa, ya yi watsi da ƙarar.

A zama na baya da aka yi, an samu halartar lauyoyin Gwamantin Tarayya yayin da lauya mai kare ɓangaren Kanu bai samu zuwa ba.

Gwamnatin Tarayya da Antoni-Janar su ne waɗanda Kanu ya zayyano a matsayin ɓangarorin da ya shigar ƙara bisa zargin tauye masa ƴanci da dokar ƙasa ta ba shi da cewa an yi garkuwa da shi daga Kenya zuwa Nijeriya don gurfanar da shi.

Ya nemi Kotun da ta bayyana dama ko dokar da ta sahale wa kawo shi Nijeriya daga Kenya.

Haka kuma ya nemi kotun da ta umarci Hukumar ƴan sandan farin kaya, ta DSS da ta sake shi, wadda ya ke tsare a ƙarƙashin ikonta da wasu ababe 11 da ya nemi kotun ta yi hukunci akan su.

By Babaji