Dalung: Kisan Filato ba rikicin manoma da makiyaya ba ne, ta’addanci ne

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni, ya bayyana kisan da aka yi a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato a matsayin ayyukan ta’addanci — ba sakamakon tsohon rikicin manoma da makiyaya ba.

A ranar Alhamis, Hukumar Raya Al’adun Bokkos  ta ce wasu da ake zargi da ‘yan fashi da makami sun kashe fiye da mutane 10 a ƙaramar Hukumar Bokkos a daren Laraba.

A ranar Asabar, rahotanni sun nuna cewa adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 52.

Harin ya faru ne kwanaki bakwai bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a yankin Ruwi na ƙaramar Hukumar Bokkos, inda jama’a suka taru don jimami a gidan mamaci.

Da yake magana a ranar Litinin a wani shiri da ake kira ‘Morning Show’ a gidan talabijin na Arise Tɓ, Dalung ya ce akwai abin da ya fi wanda mutane ke gani dangane da wadannan hare-hare.

“Babban matsala a Filato ita ce yadda ake yin kuskuren kiran masu laifi bisa la’akari da kabilanci ko dangantakar al’umma,” inji shi.

“Wannan tashin hankali ba rikicin manoma da makiyaya ba ne; ta’addanci ne. Waɗannan ƙungiyoyi suna da mafaka kamar na yankin arewa maso gabas, inda suke sace shanu, karɓe filaye da kafa wata gwamnati a daji.”

By ukarofi