Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa Nijeriya ta samu raguwar rashin tsaro da kashe-kashe da kusan kashi 90 a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ribadu ya bayyana haka ne a garin Jos na jihar Filato a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haɓen’ Manjo Janar Folusho Oyinlola a ofishinsa, biyo bayan harin da yan indiga suka kai kan al’ummar Bokkos wanda ya yi sanadin mutuwar mazauna garin da dama.
A cewarsa, gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan.
“A cikin shekaru 1-10 da suka wuce, an rage yawan da kusan kashi 90 cikin 100 a ƙasarmu.
“Muna da ƙididdigar ta shekarar 2022 da 2023, inda aka nuna cewa waɗanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunan tashin hankali a ƙasar nan sun ragu,” Mista Ribadu ya bayyana.
