Yadda Lukarawa suka kashe bijilanti 13 a Jihar Kebbi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wasu da ake zagin Lukarawa ne sun kashe wasu ‘yan bijilanti 13 a ƙauyen Morai a ƙaramar hukumar Augie a jihar Kebbi.

An kai harin ne a ranar Lahadi bayan rahotanni da ‘yan bijilanti suka samu kan yuwuwar harin tare da shirin kwantan ɓauna.

Sai dai ‘yan bijilantin ba su yi nasarar ba kamar yadda wani mazaunin garin Alhaji Augie ya bayyana wa gidan talabijin na Channels.

“Abin takaici shi ne yadda suka tarar ashe tuni ‘yan ta’addan sun zagayen su,” in ji Augie.

“A lokacin da ‘yan bijilantin suka yi ƙoƙarin buɗe musu wuta, sai su ‘yan ta’addan suka buɗe musu hutu inda suka kashe mutane 13 nan take. Kilomita 3 ne tsakaninmu da ƙauyen da wannan abu ya faru.”

Ya ce maharan sun yi ƙoƙarin satar shanu ne.

Sai dai bayan mun tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sanda, Nafiu Abubakar, ba mu same shi ba a ranar Litinin. Don haka, ba mu samu jin ta bakinsa ba.

Lakurawa ƙungiayr ta’addanci ce da ta ɓulla a jihar Sakkwato da Kebbi daga jamhuriyar Nijar da ke kai hare-haren a yankin Arewa maso yamma.

Sanatan mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, a watan Nuwambar da ta gabata, ya ce ƙungiyar Lakurawa suna amfani da muggan makamai ba tare da wani ko wasu da za su iya fuskantarsu ba.

Mista Aliero, ya taɓa zama gwamnan jihar gwamnan jihar wanda ya ce asalinsu sun taso ne daga ƙasar Mali.

“ƙungiyar Lakurawa sun sun zo ne daga ƙasar Mali kuma sun mamaye Arewacin Mali tare da bai wa gwamnatin ƙasar ciwon kai.”

“A kwanakin baya ne gwamnatin ƙasar Mali tare da taimakon dakarun ƙasashen waje ta tarwatsa ‘yan ta’addan waɗanda suka fara fashewa zuwa wasu ƙasashe ciki har da Nijeriya,” ya bayyana a lokacin zaman majalisar dattawa a yayin da yake kira ga gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki.

By ukarofi