Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Bankin Nijeriya (CBN) a ranar Asabar ya sanar da aniyarsa ta zuba Dala miliyan 197.71 cikin kasuwancin musayar kuɗin waje (Fx).
Bankin ya bayyana cewa manufar mataki shi ne samar da kuɗi da daidaita kasuwancin Dala sakamakon dokar ƙarin kuɗin harajin siyan kaya da gwamnatin Amurka ta yi.
A cikin wani jawabi da daraktan sashen kasuwancin kuɗi na CBN, Omolara Duke, ya sanya wa hannu, ya ce, matakin ya yi daidai da manufar “daidaitawa da inganta kasuwancin tsarin musayar kuɗi na ƙasashen waje.”
“A ƙoƙarin da take na tabbatar da wadatuwar kuɗi da tallafa wa kasuwanci, CBN ta tallafa wa kasuwancin musayar kuɗi da aka yi na ranar Juma’a, 4 ga watan Afirilun 2025 ta hanyar zuba Dala miliyan 197.71 wajen saye da sayarwa ta hannun dilolin da suke da sahalewar gwamnati.”
CBN ya ce ya lura da sauyin da aka samu a kasuwar musayar kuɗin waje daga ranar 3-4 ga watan Afirilu wanda ya shafi matsakaitan kasuwanci da makamantansu.
Bayanai sun daga shafin intanet na CBN ya nuna cewa a ranar Juma’a an yi musayar Dala 1 ne a kan Naira 1,567 wanda hakan ke nufin an samu faɗuwa ta kashei 1% daga bayanan da musayar Dalar da aka yi a ranar Alhamis kan Naira 1,553 na kowacce Dala 1.
“Wannan mataki na zuwa ne bayan sanarwa ta sabuwar dokar haraji da ƙasar Amurka ta ɓullo da shi kan kayan da ake shigar da su ƙasar daga sauran kasuwanni wanda ya sa aka samu sauyi a kasuwar musaya ta duniya,” a cewar sanarwar.
A ranar Laraba da ta gabata ce, shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ƙara haraji da kaso 10 na mafi ƙarancin harajin da ake karɓa kan kayan da ake shigarwa ƙasar da suka haɗa da Nijeriya wacce ke cikin ƙasashen da na su harajin ya fi yawa.
Nijeriya na shigar da ɗanyen man fetur cikin Amurka da iskar gas da takin sinadarin Naitrojin a yayin da Amurka ke sayarwa da Nijeriya motoci da tataccen mai da alƙama.
Tasirin da wannan mataki ke da shi shi ne, zai yi wa Nijeriya barazana a kasuwancinta da Amurka, musamman na ɗanyen mai wanda shi ne babban abin da Nijeriya ke fitarwa kuma da ta dogara da shi wajen samun kuɗin shiga.
A ranar Asabar, CBN ya bayyana cewa farashin man fetur ya faɗi da sama da kaso 12% inda farashin kowacce gangar mai ya dawo Dala 65.50. Wannan a cewar CBN ya zai kawo sauyi ga ƙasashe musamman masu fitar da ɗanyen mai kamar Nijeriya.
CBN ya ce zai cigaba da sa ido kan yanayin kasuwanci a cikin gida da ƙasashen waje tare da ba da tabbacin cewa Nijeriya na da ƙarfin jure wa sauyin da ake samu wajen musayar kuɗi wanda matakin da ta ɗauka zai taimaka sosai.
“Dukkan dilolin musayar kuɗin waje ana tuna musu cewa su cigaba da bin ƙa’idojin hada-hadar kasuwancin kuɗin waje da kuma bin tsari a yayin harka da abokan kasuwancinsu,” a cewar sanarwar.
