NCC ta ba wa kamfanonin sadarwa wa’adin dawo wa kwastomomi kuɗaɗen da suka cire

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar da ke Kula da Harkokin Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta fitar da sanarwar bayar da wa’adin kwanaki 90 ga kamfanonin sadarwa a wani ɓangare na wani shiri mai ƙarfi na warware matsalar da aka daɗe ana fuskanta na riƙe kuɗaɗen katin abokan ciniki.

An yi wannan sanarwar ne a yayin wani babban taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Talata, da nufin ingantawa da aiwatar da sabbin ƙa’idoji da ke kare haƙƙin abokin ciniki a fagen sadarwa na Nijeriya.

Mataimakin shugaban hukumar ta NCC, Dr. Aminu Maida, wanda kwamishinan zartarwa, gudanarwar masu ruwa da tsaki, Rimini Makama, ya gabatar da jawabinsa, ya jaddada cewa, hukumar na ɗaukar matakan da suka dace don magance abin da ke faruwa ga katin kira na layukan da ba a yi amfani da su ba, lamarin da ke shafar miliyoyin mutane a faɗin ƙasar.

“Hukumar ta himmatu wajen samar da tsarin da ya dace, wanda zai iya aiwatar da shi, kuma ya dace da kyawawan ayyuka na ƙasa da ƙasa,” inji Maida.

Ya sake tabbatar da haƙƙin abokan ciniki don dawo da katib da ba a yi amfani da su ba a cikin watanni 12.

By ukarofi