Boko Haram ta karɓe iko da garuruwa uku a Borno, inji Sanata Ndume

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Jihar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya ce mayaƙan Boko Haram sun karɓe iko da wasu garuruwa uku a jihar.

Sanatan, wanda ya faɗi hakan a yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’, ranar Juma’a, ya ce babu wata hukumar al’umma da ke yankunan, inda mayaƙan ne ke gudanar da harkokin jagoranci.

Ya ce, yankunan sune Gudumbali a Ƙaramar Hukumar Guzamala da Marte da kuma Abadam, wuraren da ya ce babu wata hukumar gwamanti da ke da iko a ɗaya daga cikin su.

Ya koka game da halin da jami’an tsaro suke a yankin, waɗanda ya ce ba a ba su wadatattun makaman da za su iya tunkarar ƴan ta’adda ba domin daƙile ayyukansu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Gwamnan jihar, Babagana Zulum ya koka game da farfaɗowar ayyukan ta’addanci a jihar, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo ɗauki.

Ndume ya ƙara da cewa, an samu ɗaruruwan hare-haren Boko Haram daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, ya na mai cewa an samu aƙalla guda 250 daga Nuwamban 2024.

Haka kuma, ya ce aƙalla sojoji 100 aka rasa da fararen hula kusan 300 duk da cewa an kashe mayaƙan 800 acikin lokacin.

Ya ce, yanzu ne lokacin da ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Borno domin tseratar da rayuka da dukiyoyin al’umma.

By Babaji