
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar Kwamitin Ayyuka (NWC) na jam’iyyar zuwa gidan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Kaduna.
Hakan ya faru ne sa’o’i bayan yawon sallar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i da Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Gabriel Suswam da wasu manyan ƴan siyasa suka je masa.
Lamarin da ya sa ake ganin ƙoƙarin taron dangi ne na ƴan siyasar Arewa akan Shugaba Bola Tinubu, yayin da zaɓen 2027 ke cigaba da ƙaratowa.
A kwanakin baya ne Atiku da El-Rufa’i suka sanar da dunƙulewa waje guda da nufin karɓe mulki a hannun Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Haka kuma ana ganin zuwan su yawon sallar a matsayin salo na ƙoƙarin janyo ra’ayin Buhari shiga cikin tafiyarsu ganin cewa gwamnatin yanzu ta fifita wani ɓangare akan ƴan Arewa musamman wajen raba muƙamai.
Saidai duk da haka, Atiku da El-Rufa’i sun yi watsi da zargin siyasantar da zuwan nasu, inda suka ce sun je wajen Buhari ne da nufin girmamawa a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ƙasa, kamar yadda suka wallafa a shafukansu na X.
