
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce duk wata haɗaka da jam’iyyun hamayya ke shirin yi da nufin kawar da APC a zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba.
Ganduje ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a yayin ziyarar da ya jagoranci shugabannin jam’iyyar wajen kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna.
Gabanin ziyarar, tawagar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar tare da tsoffin gwamnonin jihar, Mallam Nasir El-Rufai da Sanata Ahmed Maƙarfi da kuma Sanata Aminu Waziri Tambuwal da wasu, ta fara kai wa Buhari ziyara a gidan nasa.
Ya ce, ziyarar su Atiku ba ta ɗaga musu hankali ba, saboda a cewarsa, ”suna son ƙulla wata haɗaka da ba za ta yi tasiri ba”.
Ya kuma ce, ”daga abin da muka gani, mutane ne da ba za su iya haɗuwa ƙarƙashin inuwa guda ba”, inji shi.
Kazalika, Ganduje ya ce a shirye suke, kuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin kodayake ya ce ba zai faɗi dabarar da za su bi ba.
Ganduje ya ce duk da cewa a yanzu haka APC na da iko da jihohin ƙasar 21, har yanzu jam’iyyarsu na hangen ƙarin wasu jihohin, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
