Gwamna Mutfwang zai farfaɗo da ɗakin karatu na Jihar Filato don raya halayyar karatu

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

A wani ɓangare na ƙoƙarin raya ɗabi’ar karatun littattafai, da dawo da martabar ɗakunan karatu a matsayin cibiyoyin adana bayanai da bincike-bincike na ilimi, gwamnan Jihar Filato Caleb Manasseh Mutfwang ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta gyara ɗakin karatu na jihar, da samar da lambun shaƙatawa da karatu a gidan gwamnati.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake tarbar tawagar shugabannin ƙungiyar marubuta ta ƙasa reshen Jihar Filato (ANA Plateau) waɗanda suka karrama shi da shaidar jakadan littafi da adabi na Jihar Filato.

Wannan karramawa na zuwa ne a wani ɓangare na yabawa da ƙoƙarin da gwamnan yake yi na bunƙasa harkokin ilimi da inganta walwalar matasa, da cigaban zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.

A jawabinsa, gwamnan ya koka da yadda matasa suka yi watsi da ɗabi’ar karatu, saboda yaɗuwar manyan wayoyi da fasahohin zamani da suke ɗauke musu hankali daga littattafai, sai dai ya ce duk abin da za su samu na ilimi daga yanar gizo ba zai maye gurbin karatu daga littafi ba.

“Za ku iya samun amsoshin abin da ku ke nema daga waya, amma ba za ku samu cikakken ilimi ba sai a littafi. Daga karatun littafi ne ake samun ilimin gina al’umma. Idan babu masu karatu, masu rubutu ba za su samu ƙwarin gwiwa ba.” Cewar gwamnan.

Don haka ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta farfaɗo da darajar ɗakin karatu mallakar jihar da muhimman kayan karatu na zamani, yadda zai bai wa jama’a musamman matasa damar zuwa karatu da neman Ilimi, da tattauna batutuwan da za su kawo cigaban ilimi a jihar. Sannan kuma ya bayyana burinsa na samar da lambun shaƙatawa don masu buƙatar keɓewa su yi karatu ko wata tattaunawa ta ilimi, a cikin harabar fadar gwamnatin Filato.

Gwamnan ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar sa na tallafawa shirye-shiryen da ƙungiyar marubuta ta ANA take yi na bikin baje-kolin rubuce-rubuce da tattaunawa kan harkokin adabi na Jihar Filato da za a gudanar, ta yadda za a ƙawata shi ya zama abin burgewa. Sannan ya bayyana goyon bayansa wajen gayyato fitattun marubuta da duniya take yabawa da su irin su Wole Soyinka da Chimamanda Ngozi Adichie.

Shugaban ƙungiyar marubuta ta ƙasa reshen Jihar Filato, kuma shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Marubutan Adabi ta Coalition of Literary Societies, Victor Meshak ya jajentawa gwamnati da mutanen Filato bisa abin alhini da tashin hankalin da ya faru a ƙaramar hukumar Bokkos. Sannan ya bayyana ƙoƙarin da marubuta suke yi na samar da rubuce-rubuce da suke ƙarfafa zaman lafiya da raya al’adu da tarihi.

By ukarofi