Fulani sun nesanta kansu da kashe-kashen Filato

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

ƙungiyar Makiyaya ta Gan Allah Fulani Deɓelopment Association (GAFDAN), ta musanta zargin Fulani da hannu a kashe-kashen da aka yi na kwana-kwanan nan a jihar Filato.

Shugaban ƙungiyar, Garba Abdullahi ne ya ƙaryata zargin, inda ya ce an ƙirƙira maganar ce domin a ɓata sunan fulani.

“Muna jajanta wa waɗanda suka rasa ’yan uwansu, kuma muna Allah wadai da kashe-kashen. Dabbanci ne, kuma bai dace ba. 

Amma mu fulani muna faɗa da babbar murya cewa zargin ƙungiyar ci gaban al’adun mutanen ɓokkos babu tushe, zargin da suke yi na fulani na da hannu a kisan shaci-faɗi ne kawai.

“Muna kira ga ’yan Nijeriya da gwamnati da jagororin al’umma da su yi watsi da wannan zargin, domin babu hannun al’ummar Fulani a ciki”.

By ukarofi