Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ci gaba da jajircewarta na samar da kiwon lafiya da walwalar al’umma, Gidauniyar Suleiman Yahyah ta samu nasarar kai ayyukan kula da lafiya kyauta ga dubban al’umma a garin Maska da ke ƙaramar Hukumar Funtua a jihar Katsina.
Ayyukan sun ƙunshi cikakkiyar kulawar lafiya da suka haɗa da bayar da shawarwari, gwaje-gwaje, bayar da magunguna masu muhimmanci, da rigakafin cutar hanta, tare da mai da hankali musamman ga mata da yara.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban gidauniyar, Alhaji Suleiman Yahyah, ya bayyana shirin a matsayin cika aikin sa na tallafawa marasa galihu, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Yahyah ya ce “An kafa gidauniyar shekaru 16 da suka gabata don tallafa wa gajiyayyu da marasa galihu, kuma muna ci gaba da jajircewa kan wannan manufa.”
Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan kasuwa, ina bayar da gudunmawa ta hanyar zakka da shirye-shirye daban-daban na taimakon al’umma.
Taron ya samu halartar ƙwararrun likitoci daga Kaduna da Funtuwa, inda suka hidimta wa mutanen da ke fama da lalurori daban-daban.
Shirin na Maska shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin ayyukan kula da lafiya kyauta da gidauniyar ta gudanar a baya, waɗanda suka haɗa da shirye-shirye a Sardauna Crescent, ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa a shekarar 2021, da al’ummar Akko a jihar Gombe a shekarar 2022, da sauran wurare da dama.
Da yake yaba wa shirin, Hakimin Funtuwa kuma Sarkin Maska, Alhaji Mainasara Idris, ya bayyana cewa: “Wannan shiri na nuna matuƙar himma wajen gudanar da ayyukan jin ƙai, Alhaji Suleiman Yahyah mai kishin ƙasa ne kuma mai tsoron Allah, wanda kuma tausayin sa ke ci gaba da canja rayuwar mutane a Maska da sauran wurare, Allah Ya saka masa da alheri.”
Shugaban sashen kula da lafiya a matakin farko a Maska, Lawal Hamisu Maska, ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manya-manyan ayyukan kiwon lafiya a baya-bayan nan.
“Ban taba ganin fitowar jama’a irin wannan ba, yawan mutanen da aka yi wa magani, da kuma ingancin kulawar da aka bayar sun yi fice. Muna godiya ƙwarai da gaske” inji shi.
Wasu da suka ci gajiyar shirin su ma sun nuna jin daɗinsu.
Audu Hamisu Maska, wanda ya samu maganin cutar hawan jini da ulser, ya ce: “Dukkan ayyukan an yi su ne kyauta, ina addu’ar Allah ya sakawa wanda ya samar da wannan shiri da albarka”.
Aminu Ango, wani wanda ya ci gajiyar tallafin, ya ƙara da cewa: “Na samu maganin matsalar ido da ciwon mara, ba tare da ko kobo ba, Allah Ya ƙara masa ƙarfin gwiwa da arziki.
Ita ma Halimatu Alhaji Ado, wadda ta samu maganin ciwon mahaifa, ta ce: “Wannan tallafin ya zo a daidai lokacin da ban biya ko kobo ba kuma tuni na fara samun sauƙi.
