
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto wasu yara 13 da ake zargin sace su aka yi daga jihar, waɗanda aka yi safarar su zuwa Kalaba a Jihar Kuros-Riba da Enugu da Anambra da kuma Jihar Kebbi.
Kwamishinar Walwalar Al’umma da Ci-gabansu ta jihar, Rabi Salisu ta bayyana hakan a taron manema labarai.
Ta ce, da fari an kai yaran ne wani gidan marayu a Abuja, kana daga bisani wani ɗan safarar mutane ya yi jigilarsu tare da wasu zuwa wasu jihohi.
An ga yadda yaran suka shiga halin farin ciki a lokacin da aka sada su da iyalansu.
An kuma yi zargin sace su a Kaduna inda kuma aka kai su jihohin kudun da Kebbi domin sayar da su ga wasu mutane.
Gwamantin Kaduna tare da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro suka yi nasarar ceto yaran, waɗanda galibin su an sace su ne kwanaki kaɗan bayan haihuwar su.
Kazalika, ta ce an kama wasu mutane biyar da ake zargin su da hannu a laifin, waɗanda a halin yanzu suna hannun hukuma inda ake gudanar da bincike akan su.
