AFDEIC: Shugabannin fasaha za su tattauna kan tattalin arzikin dijital na Afirka a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An sanar da taron tattalin arziki na dijital na Afirka (AFDEIC 2025) kuma an shirya gudanar da shi a Abuja, Nijeriya, daga 12 zuwa 14 ga Agusta, 2025.

Ana sa ran taron zai ƙunshi jami’an gwamnati, masu tsara manufofi, shugabannin ‘yan kasuwa, masu ƙirƙirar fasaha da masana kimiyya don tattauna batun tattalin arzikin dijital na Afirka da kuma rawar da ke tattare da fasaha a yankin.

Masu shirya taron, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, sun ce taron mai taken: “ƙirƙirarriyar Basira ra AI da Tattalin Arzikin Dijital na Afirka”, zai mai da hankali kan hada-hadar kuɗi, faɗaɗa kayayyakin more rayuwa na dijital, amfani da AI, sarrafa bayanai, da tsaro ta yanar gizo.

Sun ce tattaunawar za ta binciko dabarun ɗinke rarrabuwar kawuna a Afirka, da ƙarfafa tsarin fintech, da kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa a cikin hasashen cewa tattalin arzikin dijital zai ba da gudunmawar dalar Amurka biliyan 180 ga Harajin Cikin Gida na Afirka nan da shekarar 2025 kuma za ta wuce dala biliyan 712 nan da shekarar 2050.

Nijeriya na samun ci gaba sosai wajen bunƙasa tattalin arzikinta ta hanyar tsare-tsare na gwamnati kamar ‘National Digital Economy Policy’, wanda ke mayar da hankali kan faɗaɗa hanyoyin sadarwa na yanar gizo, inganta kasuwancin yanar gizo, da inganta ayyukan hada-hadar kuɗi na dijital. Har ila yau, ƙasar tana da haɓakar yanayin fasahar ƙere-ƙere, tare da bunƙasa kamfanonin fintech waɗanda ke haifar da haɗakar kuɗi.

Duk da cewa ƙaruwar shigar da intanet na ƙara ƙarfafa matsayin Nijeriya a matsayin babbar cibiyar dijital a Afirka, wani bincike da GSMA ta gudanar a shekarar 2024 ya kuma bayar da rahoton cewa kashi 61 cikin 100 na ‘yan Nijeriya mazauna karkara ba su amfani da intanet.

AFDEIC, taron tattalin arzikin dijital na Afirka, ba kawai tattaunawa ba ne, amma taro ne inda masu ruwa da tsaki za su samar da hanyoyin da za su magance ƙalubalen dijital na Afirka tare da buɗe damar nahiyar don cimma nasarar zamantakewa da tattalin arzikin ta hanyar manufofin tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya a cikin sauye-sauyen dijital ba.

By ukarofi