Zulum ya umarci a gaggauta gurfanar da malamin da ya ci zarafin yaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umarci a gaggauta gurfanar da Bukar Modu, wanda aka gan shi a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta yana dukan wani ƙaramin yaro mai suna Bashir Gaji.

Daga umarnin gwamnan ne hukumomi suka kamo Modu a ranar Asabar a yankin Umarari da ke birnin Maiduguri.

Bidiyon ya haddasa cecekuce a kafar sadarwa ganin yadda aka samu tauye haƙƙin ƴancin yara, lamarin da ya sa aka buƙaci ɗaukin shari’a.

A wata takarda, Gwamna Zulum ya bayyana cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunci kowane irin cin zarafin marasa galihu ba, ya na mai cewa lallai yaransu suna buƙatar zama cikin aminci.

Ya kuma umarci Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci-gaban Al’umma da ta faɗaɗa hanyoyin wayar da kan al’umma musamman wajen ilmantar da iyaye da malaman gargajiya wajen horar da yara yadda ya dace.

Tuni gwamnan ya gana da yaron a Gidan Gwamnatin jihar a ranar Lahadi, inda ya sanar da bada kyautar gida ga iyalan yaron da ɗaukar nauyin karatunsa.

A halin yanzu iyalan yaron suna zama a sansanin ƴan gudun hijira na Monguno biyo bayan kashe mahaifinsa da mayaƙan Boko Haram suka yi.

By Babaji