TCN ya ƙaro sabuwar tiransfoma a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Babban Kamfanin raba wutar lantarki a Nijeriya, TCN, ya kawo sabuwar na’urar tiransfoma mai ƙarfin 300MVA a tasharsa ta Katampe dake Abuja.

Hakan zai ninka yawan wutar da tashar ke iya samar wa har sau uku, wanda ke nufin Babban Birnin Tarayya da maƙota birnin za su kara samun wadatuwar ingantaccen hasken lantarki ga ababen more rayuwa da masana’antu.

Aikin tashar wani ɓangare ne na haɗin-gwiwa da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi tsakanin TCN da Bankin Duniya don haɓaka ƙarfin rarraba wutar a Nijeriya.
Ana sa ran wannan ci-gaban zai yi tasiri sosai kan yanayin samar da wutar lantarki a Abuja.

Haka kuma ƙoƙarin da TCN ke yi na inganta hanyoyin sadarwa na kasar na samun ci-gaba.

By Babaji