Rahotannin FBI da DEA: Babu wani sabon abu – Fadar Shugaban Ƙasa game da zargin Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da hukuncin wata kotun Amurka da ke umartar hukumomin ƙasar da su fitar da bayanan sirri da suka tattaro game da binciken Shugaba Bola Tinubu na alaƙanta shi da batun ta’amali da ƙwayoyi a shekarun 1990s.

A wata sanarwa ranar Lahadi, Fadar ta ce babu wani sabon abu game da rahotannin da Agent Moss na cibiyar bincike ta FBI da na Hukumar Kula da Harkar Ƙwayoyi, DEA suka fitar, wanda abu ne da aka yaɗa wa duniya tun sama da shekaru 30 da suka gabata.

Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce rahotannin ko kusa ba su shafi Shugaba Tinubu ba, inda a yanzu lauyoyinsa sun fara nazari game da hukuncin.

A ranar Talata ne wata kotu a birnin Washington DC ta umarci FBI da DEA su fitar da rahotannin da aka alaƙanta da Shugaban Nijeriyar, lamarin da ya sa lauyoyinsa da ke Amurka, wato Babatunde Ogala da Antoni Afolabi suka fitar da wasu bayanai da ke nesanta Tinubu da abinda ake zargin nasa a kai.

Onanuga ya kuma ce tun daga shekarar 1994 Shugaba Tinubu ya ke shiga Amurka kuma an ba shi ƴancin shiga ko fita daga ƙasar ba tare da wani sharaɗi ba.

A shekarar 2023 wani ba’amurke mai suna Aaron Greenspan ya shigar da ƙara akan wasu hukumomin Amurka da daga ciki akwai FBI, DEA, CIA, IRS da ma wasu manyan manyan jami’an shari’a, inda ya ƙalubalance su da ɓoye wasu manyan batutuwan binciken da aka jingina wa Shugaba Tinubu da wani Abiodun Agbele.

Mutane huɗu da ya lissafo a matsayin waɗanda ya ke neman a fitar da sakamakon binciken ta’amali da ƙwayoyi akan su sune: Bola Ahmed Tinubu, Lee Andrews Edwards, Mueez Adeboyega Akande da Abiodun Agbele.

By Babaji