2027: APC a Borno ta nemi Tinubu ya cigaba da tafiya da Shettima

Spread the love

Dafa BELLO A. BABAJI

Jami’yyar APC a Jihar Borno ta jaddada goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takara a zaɓen 2027 tare da kira a gare shi da ya riƙe mataimakinsa, Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa a wani karon.

Ta sanar da hakan ne a wata takarda jim-kaɗan bayan kammala zama a Gidan Gwamnatin jihar na masu-ruwa-da-tsaki, ranar Lahadi.

Mai bai wa Gwamnan Babagana Zulum shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dogo Shettima ya, fitar da sanarwar inda ya ce zaman ya ƙunshi sanatoci da ƴan majalisar wakilai daga jihar, ƴan majalisar dokokin jihar, kwamishinoni, ciyamomi da wasu jigajigan APC.

Lamarin ya biyo bayan sukar da Sanata Ali Ndume ya yi wa Shugaba Bola Tinubu ne na cewa ya na nuna ɓangaranci a yayin raba muƙamai, lamarin da Fadar shugaban ƙasa ta musanta daga baya.

Saidai, duk da faruwar hakan, mambobin jami’iyyar sun nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Tinubu da Ajandarsa ta Sabunta ƙasa.

Sun kuma yaba wa mataimakinsa, Shettima, bisa ƙoƙari da jajircewarsa ga ci-gaban ƙasa da rawar da ya ke takawa wajen cimma kayawawan manufofin Shugaba Tinubu.

By Babaji