
Daga BELLO A. BABAJI
Al’amarin hare-hare a wasu yankunan Filato na cigaba da ƙamari duk da ƙoƙarin gwamnati na daƙile su, yayin da mutane 40 suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ƴan ta’adda suka kai wa garin Zike a yankin Kimakpa dake Gundumar Kwall a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne a asubahin farko na ranar Litinin, inda maharan suka farmaki ƙauyen tare da yin harbe-harbe da ya sa mutane suka yi ta ƙoƙarin tsere wa rayukansu, kamar yadda Dagacin Kwall, Wakili Tongwe ya bayyana.
Ya bayyana wa manema labarai cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da suka je sintiri tare da wasu ƴan bijilante a wani ƙauyen.
Duk da cewa daga baya sun yi yunƙurin mayar da martani ga harin, aƙalla mutane 36 ne suka rasu, kana daga bisani wasu huɗu ma suka rasu.
Ya kuma ce, wasu daga cikin waɗanda aka harba suna asibiti domin karɓar kulawa daga likitoci.
Zuwa lokacin kammala rahoton, hukumomin tsaro ba su yi tsokaci game lamarin ba.
Hakan ya faru ne ƙasa da makonni biyu da wasu mahara suka kashe mutane 52 a Ƙaramar Hukumar Ɓokkos dake jihar.
