Yadda littafin ‘Burin Salma’ ya bayyana muhimmancin ilimi a yaƙi da cin zarafin ýaýa mata 

Spread the love

Daga ALEXANDER IZANG

Gajeren labarin da Abba Abubakar Yakubu rubuta mai suna Burin Salma ya nishaɗantar da mu sosai, mun kuma koyi darussa da dama. Babban jigon da wannan labari ya ginu a kai shi ne batun mummunan halin da ‘ya’ya mata suke fuskanta a hannun azzaluman maza – wato wannan annoba da ta mamaye zaman mutuntakarmu: fyaɗe.

An fara buɗe wannan labari ne da bayyana mana yadda wata yarinya Salma ta fuskanci harin fyaɗe daga wani kawunta Bala. Kodayake bai ci nasara ba, sakamakon ƙoƙarin da ta yi wurin kare kanta da budurcinta, ta hanyar buga masa sanda; ta kuma nemi taimako ta hanyar yin ihu don jan hankalin babarta.

Wannan jarabta ta sa Salma cikin tsoro da tashin hankali; da safe ta zayyana wa babarta abin da ya faru, jin haka sai ita babarta ta ce mata za ta fuskanci kawu Bala, amma kada wannan magana ta fita daga bakin Salma zuwa wani kunnen.

Labarin ya gangara zuwa kan wata yarinya mai suna Sailuba – ƙawar Salma – wacce ita ba ta taki sa’a kamar Salma ba, sanadiyyar ibtila’in da ta samu kanta a ciki. Makwafcinta ne ya ci zarafinta ta hanyar yi mata fyaɗe. Lura da labarin da ta bai wa Salma, al’amarin ya faru da ita ne yayin da take taya mahaifiyarta sayar da koko da ƙosai. Sai dai abin takaici shi ne, bayan ta gayawa babarta abin da ya faru da ita, sai ta umarce ta kada bakin ta ya fitar da wannan magana. 

Mun karanta a cikin wannan gajeren labari lokacin da Salma take tambayar Sailuba ko ta sanar da babarta abin da ya faru? Sai ta ce, “Na gaya mata, amma ta ce in kame bakina kada kowa ya ji. Wai zan iya rasa mai aurena, za a ce ni ba cikakkiyar budurwa ba ce. Tunda wani namiji ya taɓa saduwa da ni.”

Ba a nan munin al’amarin ya tsaya ba; Sailuba ta ɗauki ciki wanda ya kai ta ga mutuwa cikin ƙuruciyarta. Ya faru ne yayin da babarta ta saka ta shan maganin zubar da ciki. A wajen maƙwafta ciwon daji ne yake damun Sailuba saboda tsananin da jikin ta ya yi, daga Salma sai mahaifiyarta kaɗai suka san asalin abin ya faru da ita.

Mutuwar Sailuba ta shuka wani iri a cikin zuciyar Salma wadda ta ɗauki niyya da alƙawarin yin yaƙi da wannan muguwar halayya da ke lalata da makomar ‘ya’ya mata. Ta yi ƙoƙari wajen jan ra’ayin wasu ‘yan mata don su haɗa kai tare da faɗakar da su hanyoyin da za su bi su kare mutuncinsu da ɗiyaucinsu. Ba tare da sun bari wani shashasha kuma azzalumin namiji ya cutar da rayuwarsu ba (mu duba shafi na 6). 

Tawagar waɗannan ýan mata ta samu abokiyar tafiya a cikin malaman makarantar su, wato Malama Amina, wacce labarin ya bayyana mana cewa ita ma ta taɓa fuskantar irin wannan muguwar halayya ta cin zarafi. Ta gaya wa Salma da ƙawayenta cewa, “Naso a ce ni ma na samu ƙwarin gwiwa tun ina ƙarama, na yi wani abu mai kama da wannan da kuke yi. Nima tun ina ƙarama, mijin babata ya min fyaɗe a gona lokacin da na kai masa abinci. Abin haushi da takaici babu abin da aka yi masa, ita babata ma sai musanta abin ta yi, don kar aurenta ya mutu. Ni kuma ta riƙa min barazana tana zare min idanu don kada na kuskura na gaya wa kowa.” (mu duba shafi na 9).

Domin bayyanar da munin al’amarin da kuma fayyace dalilan da suka sa waɗannan yara suka nace cikin wannan yaƙi da suka ɗaura niyya da masu cin zarafin ýaýa mata. Salma ta faɗa cewa, “Dukkanmu kusan sa’o’in juna ne, ba mu wuce shekaru goma sha biyu zuwa sha huɗu ba. Kuma muna karatu ne a ajin ƙarshe. Labarinmu kusan duk iri ɗaya ne, daga wacce aka ketawa haddi, sai wacce aka ci zarafi a ƙoƙarin a yi mata fyaɗe. Shi ya sa muka haɗa kai don mu ɗauki fansa kuma mu kare ƙannenmu mata masu tasowa daga wannan ɗanyen aiki da wasu lalatattun maza ke aikatawa (mu duba shafi na 10).

Wannan labari da Abba Abubakar Yakubu ya wallafa na cike da darussa masu yawa da za su amfani rayuwar mu ta yau da kullum.

– Na farko. Mun ga cewa al’amarin fyaɗe wata annoba ce da ta bazu sosai a cikin al’umma; dole ne mu ji tsoro game da makomar ýaýan mu mata.

– Na biyu. Salma da ƙawayenta sun nuna mana cewa, la’anta da yawan ƙorafi ba su wadatar ba, akwai abin da kowa zai iya yi ya taimaka don rage wannan mumunan hali.

– Na uku. Akwai buƙatar malamai kamar irinsu Amina, waɗanda za su jagoranci ɗalibai da koyar da su abin da ya dace su yi don su kare kansu da ɗiyaucinsu.

– Na hudu. Mahaifiyar Salma ta maimaita mana babban darasin da rayuwar mata (har maza ma) suke ɗauka saboda ƙuncin da suke fuskanta game da fyaɗe. A shafi na goma mun karanta abin da take cewa, “raɗaɗin da waɗanda aka yi wa fyaɗe suke ji a ransu ba ya taɓa fita daga zuciyoyinsu har abada.”

– Mai biye da shi, darasi na shida. Mun koyi cewa lallai ne iyaye su guji halin rufe bakinsu da na ‘ya’yansu yayin da irin wannan al’amari ya faru; yin shiru ne ke ƙara wa waɗannan mugayen mutane ƙwarin gwiwar cigaba da aikata wannan mummunar halayya. Gwamnati da shugabannin al’umma, musamman sarakunan gargajiya na da hakkin kare mutunci da rayuwar al’ummarsu, musamman yara mata da maza.

A ƙarshe abin tambaya shi ne, menene burin Salma? Burin Salma shi ne ta samu zarafin yin ilimi ta hanyar yin karatu, wanda shi ne yake buɗe idanun mutane da wayar musu da kai. Ta gano cewa, “Lallai ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa, kuma mata da sauran al’umma ba za su samu cimma burinsu na rayuwa ba sai sun haɗa kai sun nemi ilimi, kuma sun jajirce. ” (mu duba shafi na 11). Salma ta bi matakan neman ilimi har ladar ƙarshe, yayin da ta kai dab da matakin zama Daktan ilimi, a tsangayar nazarin fasaha. Ta cika burin nan da mahaifinta ya shuka a zuciyarta game da muhimmancin ilimi, ta tuna tun farko ya ce mata. “Ilimi shi ne fitilar da ke haskawa mutum hanya don ya fahimci rayuwarsa da abubuwan da ke kewaye da shi. Kuma ilimi haske ne mai yaye duhun jahilci.” (mu duba shafi na 4).

By ukarofi