Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Katsina sun sami nasarar kama ɓarayin mota bayan sun ƙi yarda da ƙarɓan cin hanci na Naira miliyan ɗaya.
A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar sadiq Aliyu ya ce ‘yan sandan sun kama ɓarayin ne a garin Birnin Kuka a ƙaramar hukumar Mashi.
Ɓarayin da suka haɗa da Mubarak Kabir da Adamu Hashim waɗanda mazauna Fagge a Jihar Kano sunyi ƙoƙarin ba ‘yan sandan Naira miliyan ɗaya a matsayin cin hanci amma ‘yan sandan suka ƙi amsa.
‘Yan sanda sun kama ɓarayin ne cikin wata mota ƙirar Toyota Corrola da ake zargi na sata ne.
Bincike da ‘yan sandan suka gudanar mutanen sun saci motar ne a Abuja.
Ƙarin bincike da ‘yan sandan suka gudanar sun gano wayoyin hannu guda uku da mabuɗi da ake zargin ɓarayin suna amfani da shi wajen satar ababen hawa.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar cp Bello Shehu ya jinjina wa ‘yan sandan bisa ƙwarewa da jarunta da suka nuna wajen kama waɗannan barayi.
Garin Birnin kuka yayi iyaka da ƙasar Nijar kan haka ake tsammanin ɓarayin sunyi yunƙurin fitar da motar zuwa ƙasar Nijar.
