‘Yan bindinga sun yi garkuwa da ɗan sanda, da wasu mutane biyu a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani jami’in ɗan sanda da wasu fararen hula biyu a wani harin kwantan ɓauna da suka kai a hanyar Ɗanmusa zuwa ‘Yantumaki.

Harin dai ya haifar da fargaba da razani ga mazauna yankin inji majiyar Manhaja.

A cewar wasu mazauna yankin da kuma rahotannin ‘yan sanda, waɗanda lamarin ya rutsa da su – ciki har da jami’in ɗan sanda Nura Ibrahim, a yayin da yake tafiya cikin wata mota ƙirar Golf mai ruwan shuɗi, lokacin da ‘yan bindigar suka tare su a kusa da tashar ‘Yantumaki.

Shaidun gani da ido sun ce maharan ɗauke da muggan makamai sun tilastawa motar sauka daga kan titin kafin su yi awon gaba da mutanen zuwa cikin dajin da ke kusa da wurin.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da sace mutanen tare da bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da aikin ceto na haɗin gwiwa don kuɓutar da mutanen.

Tuni dai jami’an tsaro suka karɓo motar da aka sace mutanen bayan an yi watsi da ita a wurin da lamarin ya faru, a yayin da rundunar ta baza jami’anta na sama da ƙasa don saka ido.

“Wannan aika-aikar da ake yi wa jami’an mu da kuma ‘yan ƙasa ba za mu lamunta” in ji SP Abubakar Aliyu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar.

“Mun tura duk wani kayan aiki don kuɓutar da waɗanda abin ya shafa, tare da kama waɗanda suka aikata wannan laifi.” In ji kakakin rundunar.

Har yanzu mazauna jihar ta Katsina na kokawa game da yadda ‘yan bindinga ke kai hare hare, a wasu daga cikin ƙananan hukumonin jihar duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro da gwamnatin jihar ke cewa suna yi ba dare ba rana don daƙile matsalar.

By ukarofi