‘Yan sanda a Katsina sun kama dillalan miyagun ƙwayoyi sun biyu ɗauke da ƙwayoyi na Naira Miliyan 3.5

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda a Katsina sun kama wani mutum mai suna Murtala Salisu ɗan shekaru 27 da ke ƙauyen Bare Bari a ƙaramar hukumar Safana ɗauke da ƙwayar Tramadol da aka ƙiyasta kansu zai kai Naira Miliyan 3.5.

A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan a Katsina yace wanda ake zargin ya shaidawa jami’an tsaron yana samu waɗanda miyagun ƙwayoyi daga wani mai suna Rabe da ke Jihar Nassarawa.

Murtala da ake zargi ya kuma bayyana sunan Tanimu Abubakar daga ƙaramar hukumar Jibiya a matsayin mutumin da suke sana’ar hada hadan ƙwayoyin tare.

Jami’an ‘yan sandan tuni suka kama mutanen tare da ƙwayoyin Tramadol da yawan ya kai 2000 kuma da zarar sun kammala bincike zasu gabatar da masu laifin a gaban hukumar.

Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Katsina CP Bello Shehu ya yaba da jami’an tsaron da suka nuna ƙwarewa da jarunta wajen kama waɗannan miyagun mutane.

By ukarofi