MOPPAN ta yaba wa gwamnan Kano bisa bai wa mambobinta kujerun Hajji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Ƴan fim ta Ƙasa, MOPPAN, ta jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano bisa bai wa wasu daga cikin mambobinta kujerun aikin Hajjin bana.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kakakinta, Ibrahim Amarawa, ƙungiyar ta ce hakan ya samu me sakamakon ƙoƙarin gwamnan wajen inganta walwala da jin-daɗin masana’antar Kannywood da ƴaƴanta.

Ta kuma yaba da yunƙurin gwamnan na tallafa wa harkokinta ganin yadda ta ke taimaka wa ci-gaban al’adun Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, MOPPAN ta ce tana alfahari da tsarin shugabancin gwamnan na samar da ci-gaba ga al’umma da kuma ɗaga darajar Kannywood a gwamnatinsa.

Waɗanda aka bai wa kujerun Hajjin sun haɗa da Hajiya Fauziyya D. Sulaiman, Umar UK da kuma TY Shaba.

Har’ilayau, ta yi masa fatan Allah Ya saka masa da alkhairi tare da riƙo da hannunsa wajen cigaba da ayyukat inganta jihar da masana’antar ƙirƙira a jihar.

By Babaji