Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada umarnin dasa itatuwa a manyan hanyoyin a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙokarin sa na magance kwararowar hamada, gwamna Dikko Raɗɗa ya bada umurnin dasa itatuwa a duk manyan hanyoyin da gwamnatin sa ke aikin gina wa a faɗin jihar.

Ya kuma bada umarnin a fara dasa itatuwa a hanyar shatale tale mai tsawon kilomita 23 da ake aikin ginawa a jihar.

Yace wannan dasa itatuwa a waɗannan hanyoyi zasu taimaka ba wai kawai ƙayata gari ba harma da kare kwararowar hamada.

Gwamnan ya bada wannan umurni ne a zaman taron majilisar zartarwa da ya gudana a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar.

Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da ƙarin kuɗin da gwamnatin jihar ke badawa kyauta ga waɗanda suka sami nasarar gasa akan sauyin yanayi.

Haka kuma mutum uku da suka sami nasara a gasar za a karrama su a wani babban taro da gwamnatin jihar zata gudanar a Abuja.

By ukarofi