Ana artabu tsakanin Fulani da Lakurawa a Kebbi

Spread the love

*Zarge-zarge sun fara fito wa fili a yankuna

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Rahotanni daga ɓangaren yankin ƙananan hukumomin Arewa da Augie a Jihar Kebbi na nuni da cewa, yanzu haka ana artabu tsakanin ’yan ta’addar Lakurawa da Fulani makiyaya a waɗannan yankunan sanadiyyar shigar burtu da makiyayan ke yi suna kai farmaki a waɗansu ƙauyuka suna kisan mutane a al’ummomi daban-daban.

Wani jami’in tsaro da ya ke aikin sintiri a wannan yankin, wanda bai amince a ambaci sunansa ba, ya shaida wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, sau da yawa Lakurawan sukan kashe Fulanin ne, saboda suna kai farmaki suna kisan mutane da sunan Lakurawan, wanda abin bai yi wa su Lakurawan daɗi ba.

Ya bayyana cewa, Lakurawan suna zaune da mutanen garuruwan da suke waɗannan yankunan da ke kan iyakar Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar cikin lumana, inda har suna hulɗar kasuwanci da su.

Ya bayyana cewa, mafi yawancin dalilan da suka sa su makiyayan ke kashe mutanen garin da suke kai farmaki shi ne, suna ganin mutanen garin sun san su kuma suna gane su.

Wani mazaunin ƙauyen Kwaido da ke ƙaramar Hukumar Augie ya tabbatar da haka, inda ya ce, gaskiya ne waɗannan Lakurawan suna zaune a saman tsaunuka kuma suna shigo wa ƙauyukansu suna sayayyar kayan abinci, amma dai ba su taɓa kowa. Su kan sayi man fetur, lemon kwalba, biredi da dai sauran kayan masarufi.

Ya ƙara da cewa, shi da kansa su kan sayi kaya a hannunsa a wajen da ya ke kasuwanci a ƙauyensu.

ɗaya daga cikin ’yan sa kai daga ƙaramar hukumar Augie, wanda bai so a bayyana sunansa ba, saboda dalilan tsaro, ya tabbatar da haka, inda ya ce, yanzu haka sun sha alwashin duk lokacin da aka sake kawo musu farmaki, lallai babu gudu babu ja da baya, saboda sun fahimci ba Lakurawa ba ne ke kisan mutane, Fulanin ne, saboda akwai wani lokaci da suka taɓa yi musu kwanton ɓauna a yayin wani hari, inda suka kashe mutane 18, amma akasarinsu Fulani ne da aka sani.

Sai dai wani abin damuwa shine, za ka ga an tara shanun mutane duk da cewa a kan bi sawun waɗannan ɓarayin sai duk shanun su yi ɓatan dabo a cikin ƙanƙanin lokaci a rasa inda suka bi, wanda ya sanya mutane da yawa zargin hukumomi, saboda hana su bibiyar sawu, sannan ita kuma hukumar ba abinda ta ke yi sai dai ka ga jiragen sojoji suna kara-kaina a sararin samaniya.

Haka zalika yanzu an soma gano waɗansu shanu da aka sace a kasuwanni da kuma gidajen waɗansu mutane da ke da alaƙa da fawa a cikin waɗansu manyan birane ko kuma idan aka canja wa wani babban jami’in tsaro wajen aiki, sai ka ga an cika manyan motoci da shanu wai nasa ne.

Malam Muhammad Sha’ban, wani malamin addinin Musulunci a yankin, ya nuna damuwarsa bisa irin yadda hukumomi kuma wai zaɓaɓɓu ke ko oho da nauyin da ke rataye a wuyansu, saboda neman abin duniya, inda ya ta’allaƙa wannan ta’addanci ga hukumomi saboda rashin samar da tsaro ingatancce.

Ya ƙara da cewa, duk abinda mutum ya aikata ba shakka abin tambaya ne ranar ƙiyama, saboda haka su ji tsoron Allah su samar da tsaro ingatancce ga al’ummar da suke wakilta.

By ukarofi