Nijeriya ta tsallake yayin da Trump zai rufe ofisoshin jakadancin Amurka a Afrika

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump na yunƙurin rufe ofisoshin jakadancin ƙasar dake Afirka da wasu yankunan duniya, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Kimanin ofisoshi 30 da wasu cibiyoyinta a sassan duniya za a rufe a ƙoƙarin gwmantin na rage adadin shigarta harkokin difulomasiyya a ƙasashen waje.

Ofishin harkokin cikin gida na ƙasar ya ce daga cikin na ƙasashen da za a rufe akwai Jamhuriyar Congo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Lesotho da Kudancin Sudan da cibiyar tuntuɓa ta Afirka ta Kudu.

Haka kuma akwai wasu ofisoshin jakadancin a Turai, Asiya da yankin Caribbean da sauran su.

Kawo yanzu ba a samu tabbatarwa daga Sakataren Amruka, Marco Rubio ba ko wani jawabi daga kakakin ofishin ba.

By Babaji