NDLEA ta kama wasu bisa safarar tabar ibilis cikin litattafan addini zuwa Saudiyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), sun yi nasarar kama wasu ƙullin hodar ibilis guda 20 acikin littatafai da aka nufi kai su ƙasar Saudiyya.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya faɗi hakan a wata takarda a ranar Lahadi, inda ya ce sun gano hakan ne daga wani kamfanin jigilar kayayyaki a Legas a ranar 15 ga watan Afrilu, 2025 yayin binciken kayan da za a yi safarar su zuwa ƙasar.

Haka kuma a ranar ne suka kama tabar wiwi mai nauyin kilogram 2.8 a hannun irin kamfanin, wanda aka yi jigilar sa daga Amurka.

A Jihar Kano kuwa, jami’an sun kama wani mai aikin raba miyagun ƙwayoyi, mai suna Muhammad Muhammad ɗan shakara 22 a lokacin da ya nufi Jihar Katsina da allurar ‘ampoules pentazocine’ guda 277, wanda ya ɓoye su a cikin wandonsa.

Haka kuma, jami’an sun kama Mohammed Abdurrahman Abdul’aziz mai shekaru 43 da wasu kayan maye da tabar wiwi a Rimin Kebe dake Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.

Har’ilayau, a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa NDLEA ta kama wasu mutum huɗu a yayin wani same a wani gida dauke da wasu nau’ukan kayan maye da dama, a yankin Opolo.

Sauran Jihohin da jami’an hukumar ta kama masu laifuka sun haɗa da Kebbi, Edo da kuma Legas a atisaye daban-daban, lamarin da ke nuna yadda hukumar ke ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’amali da miyagun ƙwayoyi acikin al’umma a Nijeriya.

By Babaji