Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Malam Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka a lokacin da yake hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce an kashe waɗannan kuɗaɗen a wajen ɗauka,horar wa tare da samar da kayayyakin aiki ga rundunar tsaro da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ƙirƙiro KCWC.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da motocin aiki,babura, na’urorin sadarwa,na leƙen asiri tare da tattara bayanai,makamai domin tallafawa jami’an wajen aikin su.
“Wannan gwamnati ta rungumi hanyoyi biyu na amfani da ƙarfi da kuma jawo hankali tare da tallafawa al’umma da matsalar ta shafa don inganta matsalar tsaro a jihar”inji Malam Farouk Joɓe.
Mataimakin gwamnan ya bayyana wasu tsare tsare da manufofi da gwamnatin jihar ta aiwatar da suka haɗa da kirkiro da ma’aikatar kula da sha’anin tsaro da al’amuran cikin gida.
Sauran sun haɗa da kafa rundunar tsaro ta al’umma wato KCWC da ɗaukan limamai da na’ibai da ladanai guda 7,545 don gudanar da addu’a da wa’azi tare da nasiha kan mahimmancin zaman lafiya.
Haka kuma gwamnatin jihar ta ɗauki masu unguwanni 6,652 don sa ido kan sha’anin tsaro inji malam Joɓe.
Gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kuma ɗauki mutane fiye da 10,000 a matakin ƙananan hukumomi da masu unguwanni wajen wayar da kan jama’a kan mahimmancin zaman lafiya inji Joɓe.
Duk dai a cikin wannan kuɗaɗen da gwamnati ta kashe wajen sha’anin tsaro, ta ɗauki jami’an tsaron al’umma da yan sintiri da mafarauta da a duk wata gwamnati na biyan su alawus bayan da samar masu da kayan aiki.
Da dai sauran matakai da dama da gwamnatin jihar ta ɗauka na tanadar wa jami’an tsaron kayayyakin dabarun yaƙi yace.
Mataimakin gwamnan ya ce duk wannan matakai da gwamnati ta dauka ya haifar da kyawawan sakamako , da dawo da zaman lafiya a yankunan da a baya ƴan bindiga suka tarwatsa.
