Oyo: Mai gyaran wutar lantarki ya rasu a yayin gyara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Lamarin ya auku ne a ranar Laraba, inda wani ɗan shakara 28 da ke aikin gyaran wutar lantarki ya gamu da ajalinsa a yayin da wayar wuta ta ja shi a yankin Eruwa na Karamar Hukumar Ibarapa ta Gabas a Jihar Oyo.

An ruwaito cewa nan take mai gyaran wutar ya rasu a lokacin da ya ke ƙoƙarin gyara wani tsaiko da wutar yankin ta samu a wani babban layin lantarki.

Haka kuma an gano cewa, ya fara aikin ne ba tare da an kashe wutar daga makunninta ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Janar Manaja na Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Akinyemi Akinyinka ya ce, sun samu labarin aukuwar lamarin ne bayan kiraye-kiyare da aka yi masu, yayin da a lokacin da suka kai ɗauki, suka samu har ya rasu.

Tuni dai suka sanya matakan kariya a yankin don ƙaurace wa sake aukuwar irin al’amarin.

Ya kuma ce, sun kai wa jami’an ƴan sandan yankin da abin ya faru gawar mamacin.

By Babaji