APC ba ta da niyyar maida Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba – Sanata Bashiru

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sakataren Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya yi watsi da iƙirarin da ake na cewa jam’iyya mai mulki ce ke jagorantar Nijeriya wajen tafiyar da tsarin jam’iyya ɗaya.

Sakataren jam’iyyar ya bayyana hakan ne a gidan Talabijin na Channels Tɓ’s a shirin Politics Today a ranar Laraba, inda ya kare harkokin siyasar jam’iyyar APC tare da yin watsi da shawarwarin da gwamnati ke yi wa jam’iyyun adawa.

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Delta Sheriff Oboreɓwori, mataimakinsa, Monday Onyeme, da kuma tsohon gwamna Ifeanyi Okowa suka sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam’iyyar All Progressiɓes Congress, tare da kwamishinoni da masu ruwa da tsaki a jihar.

Da aka tambaye shi ko ya damu da yadda ake ƙara fahimtar cewa jam’iyyar APC da gwamnati mai ci na mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya, sai Basiru ya mayar da martani.

“Ta yaya za mu mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya?” Ya tambaya. “Kasan ba mu ne suke yi ba, manufofin ƙasar ba mu ne suke yi ba.

“Ina ganin matsalar da ke damun Nijeriya ita ce, kamar ba mu da mutane masu kishin adawa, waɗanda ke ɗaukar aikinsu da muhimmanci. Ba za ka iya tsammanin jam’iyya mai mulki za ta yi aikin ‘yan adawa ba.”

Da yake ƙalubalantar kafafen yaɗa labarai, Basiru ya buƙaci ‘yan jarida da su tantance gazawar jam’iyyun adawa, inda ya kwatanta hakan da ƙoƙarin da jam’iyyar APC ke yi na gina katafaren tsari, mai tushe a faɗin ƙasar nan.

“Gobe ranar aiki ce — ku zaga hedkwatar sauran jam’iyyun siyasa ku gani ko kun ga wani aiki yana gudana.

“ɗaya daga cikin manyan manufofin jam’iyyar mu tun lokacin da Abdullahi Ganduje ya karɓi ragamar shugabancin jam’iyyar ita ce gina tsarin jam’iyya mai inganci a kowace shiyya, da ƙananan hukumomi, da jihohi a Nijeriya, kuma abin da muke yi ke nan,” inji shi.

Da yake ƙarin haske kan abubuwan da jam’iyyar APC ta samu a baya, Basiru ya tuna cewa lokacin da jam’iyyar ke adawa, ta ci gaba da dagewa a siyasance duk da matsin lamba da bincike.

“A lokacin da muke adawa – misali, Bola Tinubu, a yankin Kudu maso Yamma, shi ne gwamna ɗaya tilo da ya tsira bayan zaɓen 2003. Ko da azzaluman da mutane ke magana a kai, a yanzu mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya ce gwamna na wancan lokacin shi ne ya fi kowa binciken da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC).

“Bayan ya bar ofis, an gurfanar da shi a gaban kotun ɗa’ar ma’aikata, inda aka yi masa cikakken shari’a, bai bar jam’iyyar ba, a’a, mun tashi daga wannan jiha zuwa waccan, muna ƙoƙarin faɗaɗa ayyukanmu.”

Da yake mayar da martani kan zargin cewa jam’iyyar APC na amfani da na’urorin gwamnati da jami’an tsaro wajen tursasa ‘yan adawa, Basiru ya jawo kalaman don sauyi na Afirka Amílcar Cabral.

Sakataren jam’iyyar ya ce, “Duba, Amílcar Cabral ya ce: ‘Kada ku faɗi ƙarya, ba za ku yi nasara ba cikin sauƙi.’ Lokacin da kuke jam’iyyar adawa kuma kuka fara yi wa kanku ƙarya game da abin da ke damun jam’iyyarku—kuma ku ɗora laifin a inda ba nasa ba— uzuri ne kawai kuke yi.”

Ya ci gaba da kawo koma bayan da aka yi a baya-bayan nan a matsayin shaida kan iƙirarin cin zarafi.

“Kafin yau aƙalla ‘yan majalisar wakilai 15 daga Labour, SDP, PDP, NNPP, da sauransu sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, wasun su na farko ne, ko sun yi shekara biyu ne, ko suna da matsala da EFCC?

Sanatoci uku da suka haɗa da Sanata Ifeanyi Ubah su ma sun koma APC.

“A yau ne Honorabul Wale Oke daga mazaɓar Oriade/Obokun ya sauya sheƙa, shin a cikin waɗannan mutane akwai wanda ke da shari’ar EFCC ko ICPC?” Sakataren ya bayyana.

By ukarofi