CIGIYA: Tun jiya da rana ya bar gida, har yanzu babu labarinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ana cigiyar Salim Ibrahim (Jada), wanda ya bar gida tun jiya Alhamis, a Rukunin Gidaje na Nursing Estate dake kusa dake garin Maraba a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Wayar da aka yi da shi ta ƙarshe ita ce tun a yammacin ranar.

Ya fita da baƙar mota kirar BMW 528, mai ɗauke da lambar rijista kamar haka: GWT-846-AA, Kaduna.

Don Allah duk wanda ya samu labarin inda ya ke, ya tuntuɓi ɗaya daga cikin waɗannan lambobi: 08062084198 ko
08108049300

Don Allah a taya mu yaɗawa (sharing) ko za a dace.

By Babaji