Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, da magabacinsa, Bello Matawalle, sun yi musayar kalamai kan ƙalubalen tsaro da sauran matsalolin tattalin arziki da suka dabaibaye jihar.
Musamman rikicin da ya kunno kai tsakanin Lawal da Matawalle, ƙaramin Ministan tsaro, ya taso ne bayab wata hira da gidan talabijin a lokacin da Gwamna Lawal ya tuhumi magabacinsa kan irin shugabancinsa a jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, tsohon kwamishinan yaɗa labarai a ƙarƙashin Matawalle, Ibrahim Dosara, ya zargi Lawal da zargin cewa shi ne ke da alhakin matsalolin tsaro da aka kasa magance shi da kuma matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da jama’a ke fuskanta.
Tsohon kwamishinan a mulkin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya ce babu gaskiya cewa Dauda Lawal ya samu jihar a lalace.
Dosara ya bayyana wannan ikirari a matsayin “ba gaskiya ba” da bai kamata mutane su amince da ita ba.
A martaninsa, ya ce, “Mun shiga cikin lamarin ne saboda gwamnatinmu ta ƙarƙashin tsohon gwamna Bello Matawalle, ta yi fama da zargi mara tushe daga Gwamna Dauda Lawal.”
“Wannan ƙarya ce tsagwaron gaske. Domin tabbatarwa, tsohon gwamna ya bar biliyan N14 na bashi, biliyan N2.6 daga Bankin Duniya da biliyan N6.3 na tallafin hukumar UBE.”
“Haka kuma akwai biliyan N2.7 daga tallafin ‘NG Cares’, wanda ya samar da ribar N42bn ga gwamnatin Lawal.”
Dosara ya ƙara da cewa tsohon gwamnan ya bar bashin albashi na wata uku kacal, saboda rashin isasshen kuɗin shiga da jihar ke samu.
Tsohon kwamishinan ya yi kokwanton zargin Dauda Lawal cewa akwai rabin albashi a tsarin ma’aikatan gwamnati a jihar.
Ya ƙara da cewa, “Ina kokonto ko akwai rabin albashi a tsarin ma’aikatan gwamnati, tsarin bai kai yadda aka bayyana ba.
“Domin bayyana gaskiya, an samu bashi na wata uku ne saboda tun kafin karɓar mulki, Lawal ya hana bankuna hulɗa da gwamnatin da ta shuɗe.”
A halin da ake ciki, da yake kare kansa, Lawal ya zargi Matawalle a ranar Litinin, da kasancewa ma’aikacin gwamnati da bai iya aikin gwamnati ba, wanda ya “kasa sarrafa dukiyar ƙasa a lokacin da yake gwamna a jihar.”
Lawal, a cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai da sadarwa na gidan gwamnatin Zamfara, Nuhu Salihu Anka, ya fitar, ya ce gwamnatinsa na bunƙasa jihar sannu a hankali.
“A halin yanzu al’ummar jihar suna lura da ayyukan ci gaba a karkara da birane, garin Gusau, babban birnin jihar, yanzu ɗasawa kuma tana fafatawa don haɗa kafaɗa da wasu muhimman biranen ƙasar nan,” inji Anka.
“Ina so in ba Dosara da mai karɓar albashin sa shawara su daina ɓata lokacinsu, domin babu wani kamfen na zage-zage da za su iya hana Gwamna Dauda Lawal aiwatar da ayyukan da suka shafi jama’a.
“Ya fara da kyau, kuma da yardar Allah zai gama da kyau a wa’adin mulki na ɗaya da na biyu, Dauda Lawal ya zo aikin ceto ne, kuma al’ummar jihar sun fara samun ribar dimokuraɗiyya.”
