’Yan bindiga sun ɗora wa al’ummar Zamfara harajin miliyan N60

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

’Yan bindiga sun saka harajin Naira Miliyan 60 a kan wasu al’ummomi 12 a ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun sanya harajin ne domin su hukunta al’ummar yankunan bisa zargin bayar da bayanai ga sojoji.

Rahotanni sun ce sojoji sun kai hari a maɓoyar ‘yan ta’addan a dajin Dan Kurmi a makon jiya, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama.

Mazauna garin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun umurci mazauna garuruwan Koloma, ɗan Hayin Zargado, Zargado, Dan Godabe, Sabuwar Tunga, Makini, Bubaka, Yelwa, Bahwada, Koda, Manya, da Kabusu da su biya Naira miliyan 60 don gudun kada a kai musu hari.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun gayyaci shugabannin ƙauyukan da wakilansu zuwa wani taro domin tattauna yadda za a zauna lafiya amma ‘yan ta’addan sai suka sanya haraji a ƙauyukan a ƙarshen taron sulhun.

Wani basaraken gargajiya a garin ɗan Kurmi, Sani Usman ya shaidawa BBC Hausa cewa ‘yan ta’addan sunyi barazanar azabtar da mutanen da suka ƙona dazuzzuka a maɓoyarsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar a ƙoƙarin jinta bakinsa kan lamarin hakan ya ci tura a lokacin hada wannan rahoton.

Hakazalika, ‘yan bindigar suna cigaba da sanya haraji ga al’ummomin yankunan Jihar Zamfara da jihohin da ke makwabtaka da ita.

By ukarofi