Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugaban Hukumar Raya Kogin Rima, Alhaji Abubakar Garin Malam, ya sha alwashin samar da wadataccen ruwa ga masu noman rani da suke noma a fadamomin kusa da kogin Rima.
Ya yi wannan bayanin ne a garin Argungu a ƙarshen makon da ya gabata a ziyarar da ya kai wa manoman rani a garin Argungu.
Gari Malam ya ce, hukumar ta sami ƙorafin manoma dangane da barazanar ƙarancin ruwa a wannan kogin, wanda ba manoma kaɗai ya shafa ba har ma da kifayen da ke ciki musamman a yankunan da ke da tsaro kamar Matan Fada inda ake gudanar da bikin kamun kifi na ƙasa da ƙasa kowace shekara.
Ya ƙara da cewa, wannan hukumar tun lokacin da ta sami wannan ƙorafin ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an sako ruwa daga madatsar ruwa ta Goronyo da kuma Bakalori.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa In Sha Allahu ba za a sake samun irin wannan barazana ba har zuwa saukar damina.
Ya bayyana wannan a matsayin abin damuwa ne babba saboda dubban al’umma ke amfana da wannan kogin tun kama daga jihar Zamfara da Sokoto da Kebbi har zuwa inda ya haɗu da kogin Neja wanda bayan aikin gona akwai waɗansu mutane da suka dogara da shi wajen gudanar da sana’o’i daban-daban da suka haɗa da kamun kifi wanda hasali ma wannan kogin ya yi suna a faɗin duniya, babu inda ba a san shi ba sanadiyyar bikin kamun kifi na Argungu saboda haka ba za a bari hanyoyin neman abincin su mutu ba.
Shugaban ɗaya daga cikin ƙungiyoyin manoma na ƙaramar Hukumar Mulki ta Argungu Malam Sani Dan Manga a madadin sauran ƙungiyoyin ya yaba wa Abubakar Gari Malam bisa rashin wargantawa a lokacin da ya sami labarin wannan matsalar, inda ya ce gaskiya muna godiya ga wannan hukuma saboda inda aka fito hankalin manoma ya tashi saboda ganin irin asarar dukiyoyi da sanadiyyar rashin ruwan zai haifar sai ga shi ya zo da kan sa ya ganewa idon sa kuma tare da ɗaukar matakin gaggawa na sako ruwa da kuma alƙawarin in Sha Allahu ba za a sake samun ƙarancin ruwa a wannan kogin ba.
Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris bisa ga kulawar da ya ke baiwa talakawa musamman manoma sai dai ya yi kira ga gwamnan da ya sake fasalin rabon tallafi musamman abinda ya shafi manoma saboda sai da su ji ana cewa gwamna ya bai wa manoma kayan noma amma maganar gaskiya kayan ba sa isa ga manoma, yana makalewa ne ga waɗannan mutanen da ke ikirarin manoma ne da ke iso ga gwamnati.
“Sau da yawa mu ke jin an ce an baiwa manoma kayan noma amma babban abin ban haushi a maimakon ya zo ga manoman, a’a sai dai mu tsince shi a kasuwa” inji shi.
