Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar tuntuɓa da bada shawarwari a siyasance ta NDC ƙarkshin shugabancin Kwamared Muhammad Muhammad Inuwa wato Network For Democratic Consultation (NDC), ta shirya taro domin wayar da kan jama’a akan illar lalata fitilun kan hanya a cikin birni da yankunan karkara da ma sauran kayayyaki da gwamnatin ta samar a birane da yankunan ƙarkara wanda hakan ke da matuƙar illa wajen cigaban al’umma da birane wajen samun koma baya a ƙokarin da gwamnati na inganta rayuwar al’umma a kodayaushe kamar dai yadda shugaban NDC Kwamared Muhammad Muhammad Inuwa ya bayyana a wurin taron da ya gabata a ma’aikatar sufuri da ke Goron Dutse a ranar Asabar da ta gabata a birnin Kano.
Taron wanda ya samu gayyatar masana da shugabanni da suka gabatar da jawabai da takardu daga cikin dai masana da aka gayyata suka halarci taron ko ta hanyar wakilci akwai kwamishinan samar da wutar lantarki na jihar Kano Dakta Gaddafi Sani sai kuma kwamishinan lura da zirga-zirgar ababen hawa da harkar sufuri a Kano Hon Ibrahim Ali Namadi Dala akwai Dakta Auwalu Dansule BUK haka kuma akwai Injiniya Jibril Isyaku Sani, Malam Habibu Madigawa daga hukumar ma’aikata, Dakta Aminu Danbuzu BUK da dai sauransu.
Shi dai wannan taro an yi dogon bayani akan yadda abubuwa su ke canzawa daga wannan lokaci zuwa lokaci musamman irin fitilu na kan hanya da ake da su a Nijeriya da ma ƙasashen duniya da ma yadda suke aikin su ta yadda amfani da su zai daƙile lalata su musamman masu aiki da na’ura ta tsaro a jikin su inda guda daga cikin mahalarta taron Malam Habibu Umar ya bayyana cewa yanzu haka gwamnatin Kano ta samar da wutar lantarki mai zaman kanta wanda Kwalejin Sa’adatu Rimi da cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko ɗangote da ke titin Zaria da sauran gurare na amfana daga wannan wuta ta Tiga ta gwamnatin Kano kuma zaa cigaba da faɗaɗa wannan aiki a zamanin gwamna Abba Kabir Yusuf.
A ƙarshe shugaban NDC Kwamared Muhammad Muhammad Inuwa ya yaba wa Gwamnan Kano kan irin haɗin kai da goyan baya da yake baiwa wannan ƙungiya musamman akan tarurukan da ta ke shiryawa na wayar da kan jamaa akan abubuwa mahimai da suka shafi cigaban Kano da alummar ta wanda irin wannan taro shi ne karo na uku ta shirya kan wayar da kan jama’a don samun cigaba da gwamnati Kano ke ƙokarin kawo wa ko da yaushe inda kuma ya yabawa mahalarta taron musamman shugabanni ko kuma waɗanda suka wakilce su a wannan taro na NDC Kano.
