Shugaba Tinubu ya amince da ware biliyan N15 don tunkarar ambaliya – Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware kuɗi har Naira biliyan 15 ga Hukumar bada da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) don shirye-shiryen tunkarar ambaliyar ruwan sama da ka-iya faruwa a daminar bana.

Haka kuma ya ce gwamnatin ta kammala shirye-shiryen da suka wajaba wajen ƙaddamar da wani shiri da zai daidaita farashin kayan abinci da haɓaka harkar noma don inganta tattalin arziƙin ƙasa (NAPM).

Shettima ya furta waɗannan kalamai ne jiya Juma’a a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin taron da ya gudanar da kwamitin shugaban ƙasa da zai kula da harkokin abinci.

Ya kuma ce, shirin zai haɗa hannu da gwamnatoci wajen ingantawa tare da samar da wadataccen abinci ga al’umma a Nijeriya.

By Babaji