Mutum 25 sun mutu yayin da sama 800 suka jikkata a Iran bayan fashewar wasu sinadarai

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Aƙalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da 800 suka jikkata a wani fashewar wasu sinadarai masu haɗari da ya auku a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaei da ke birnin Bandar Abbas a kudancin ƙasar Iran, kusa da mashigin ruwa na Hormuz, inda kusan kashi ɗaya bisa biyar na fitar ɗanyen man duniya ke wucewa.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran, IRNA, ya ruwaito cewa, fashewar ta samo asali ne daga wata wuta da ta tashi a wurin ajiye kayayyaki masu haɗari da sinadarai a tashar.

Ofishin kwastam na tashar ya bayyana a cikin wata sanarwa da gidan talabijin na gwamnati ya yaɗa cewa, wutar da ta ɓarke a wurin adana sinadarai mai haɗari ita ce ta haddasa mummunan fashewar.

By ukarofi