Rikicin sarautar Kano ya kara caɓewa bayan da Sarki Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban yayansa kuma Wamban Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, kwanaki kaɗan bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Mannir Sanusi a matsayin Galadima.
Naɗin da Aminu Ado Bayero ya yi an bayyana shi cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 21 ga Afrilu, 2025, wadda babban jami’in gudanarwa, Awaisu Abbas Sanusi, ya sanya wa hannu, inda aka gayyaci Sanusi Ado Bayero ya halarci fadar Nasarawa ranar 2 ga Mayu, 2025 domin naɗin nasa.
Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda aka dawo da shi kan gadon sarauta a watan Yuni 2024 bayan rikicin siyasa, ya amince da naɗin Mannir Sanusi bayan rasuwar tsohon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya rasu a watan Maris 2025 bayan doguwar jinya.
Mutuwar Alhaji Abbas Sanusi ta bar babban gurbi a cikin manyan muƙaman masarautar Kano, inda muƙamin Galadima ke da matuƙar muhimmanci.
Waɗannan naɗin muƙamai daga sassan Sarakunan Kano biyu sun ƙara jefa masarautar cikin ruɗani yayin da ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli domin tantance sahihin Sarkin Kano.
