Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Da safiyar wannan Litinin ɗin da ta gabata ne fadar ɓatican ta sanar cewa, da misalin ƙarfe 7:35 na safe, Fafaroma Francis, wanda sunansa na asali shine Cardinal Jorge Mario Bergoglio, ya rasu a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke gudanar da bikin Ista.
Ya rasu ne washegarin ranar da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
An haife shi a Buenos Aires a ranar 17 ga Disambar shekarar 1936, inda iyayensa suka yi ƙaura na Italiya, Jorge Mario Bergoglio ya tsunduma harkokin addinin Kirista tun yana ƙarami.
Ya yi karatu a Argentina, daga baya kuma a Jamus kafin a naɗa shi a matsayin limamin Jesuit a 1969.
Ba kamar yawancin jiga-jigan fadar ɓatican ba, ya zauna a ƙasashen duniya a farkon rayuwarsa, inda ya shafe mafi yawan lokutansa a Argentina, inda ya sami suna a matsayin shugaba mai gaskiya, mai tsananin kishin ƙasa mai himma ga adalci.
Lokacin da yake matashi, ya kamu da cutar huhu mai tsanani kuma ya rasa wani ɓangare na huhunsa na dama. Duk da haka, ya kasance mai motsa jiki kuma daga baya ya zama Archbishop na Buenos Aires a 1998.
A matsayinsa na Cardinal, Bergoglio an san shi da salon rayuwa mai sauƙi, sau da yawa yana shiga notar haya ne maimakon amfani tasa.
Wa’azinsa akai-akai yana magana ne akan rashin daidaito da gwagwarmayar talakawa, yana sukar gwamnatocin da suka kasa kare masu rauni. An ana ganinsa a matsayin muryar jama’a.
Ba a taɓa samun wani fafaroma daga wata nahiya ba bayan Turai, tun bayan mutuwar Fafaroma Gregory III wanda aka haifa a Syria a shekarar 741.
Magabacinsa, Fafaroma Benedict ɗɓI shi ne fafaroma na farko da ya yi ritaya daga kan muƙamin don ƙashin kansa a tsawon shekaru 600.
Ya zaɓi sunan Francis ne don girmama St. Francis na Assisi, wani fafaroman ƙarni na 13 wanda aka sani da sadaka da kyautatawa ga dabbobi.
Ya yi karatun falsafa kuma ya sami digiri na biyu a cikin Chemistry daga Jami’ar Buenos Aires. Ya koyar da adabi, ilimin halin ɗan Adam, falsafa, da tiyoloji kafin ya zama Archbishop na Buenos Aires, babban birnin Argentina.
Wasu daga cikin abubuwan da suka sa Fafaroma Francis ya yi fice a tarihi:
Nuna adawa a fili ga wasu daga cikin manufofin Donald Trump:
Ya yi Allah wadai da yunƙurin Trump a mulkin sa na farko na gina katanga tsakanin Amurka da Meɗico, inda yace hakan ba ɗabi’ar Kiristoci bace.
Ya kuma yi Allah wadai da shirin maida baƙi ƙasashen su, da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin yi a mulkin sa na biyu.
Sunbatar ƙafafuwan fursunoni:
Fafaroma Francis ya wanke tafin ƙafafuwan wasu fursunonin gidan yarin Rome, tare da sunbata, abun da ya ja hankalin duniya.
Kira a magance matsalar sauyin yanayi:
Fafaroma Francis ya zargi manyan ƙasashen duniya da ƙin ɗaukar matakan kare muhalli da sauyin yanayi, inda a 2023 ya ce wasu matsalolin ba za su taɓa gyaruwa ba.
Jawo masu ɗabi’ar auren jinsi a jiki:
Duk da kakkausan suka da ya sha, wasu na ganin yana da ƙoƙarin jawo masu raunin imani a jiki, ciki kuwa har da yarda da ya yi ake sanya albarka ga auren jinsi.
Shi ne Fafaroma na 266, kuma na farko daga nahiyar Arewa da kudancin Amurka:
Asalin iyayen sa ’yan Italiya ne, da suka yi ƙaura zuwa Argentina. An haife shi a Buenos Aires, ranar 17 ga watan Disamba, 1936.
Ya yi kakkausar suka ga kamfanonin ƙera makamai:
Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su rungumi masalaha wajen magance rigingimu, gudun kada rikice-rikice su haifar da yaƙin duniya na 3.
Ya alaƙanta kwararar ’yan ci rani zuwa Turai, da tauye ci gaban ƙananan ƙasashe:
Ziyararsa ta farko, Francis ya je tsibirin Lampedusa, yankin da ’yan ci rani suke bi wajen shiga nahiyar Turai, inda ya ɗora laifi kan yadda ake tauye ci gaban ƙananan ƙasashen duniya.
Yana son nishaɗi irin na ƙwallon ƙafa da kuma waƙe-waƙe:
Fafaroma Francis shine Paparoma da yafi mu’amala da matasa, wajen sauraron su, da kuma ƙaunarsa da ƙwallon ƙafa.
