Daga BAKURA MUHAMMAD
Ziyarar bazata da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai wa tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da kuma tagomashi da jirgin haɗakar ‘yan siyasa ya ke samu, da alama hakan yana yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu barazanar ɗaukar wasu wajiban matakai, da suka haɗa da yi wa gwamnatinsa garanbawul, da ya haɗa da zubar da wasu cima-zaunen shugabannin hukumomin Gwamnatin Tarayya, da yi wa jam’iyyarsa ta APC canjin shugabanni.
Wata majiya makusanciyar tsare-tsaren zaɓen shekarar 2027 da ke Fadar Shugaban ƙasa, wacce ta sakaye bayyanar da kanta, ta ce tun daga wannan lokacin take nazarin ziyarar ta Atiku zuwa wajen Buhari, a garin Kaduna inda har ma suka shiga mota ɗaya zuwa sallar Juma’a lokacin ziyarar.
Kamar yadda majiyar ta ruwaito, fadar shugaban ƙasa tana cikin tsaka mai wuya sanadiyyar samun ɓaraka a gungun ‘ya’yan jam’iyyar CPC, kamar yadda tsohon babban lauyan gwamnati, kuma tsohon ministan shari’a na tarayyar Nijeriya, Abubakar Malami ke nuna bijirewarsa ga sake zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.
Bisa fafutukar samun mafita daga cikin wannan hayagaga, majiyar ta fadar shugaban ƙasa, ta bayyana cewar, fadar tana ɗaukar matakai na yin babban garanbawul kan gudanar da gwamnatin ta Tinubu ta yadda za a shigo da wasu ‘yan ‘siyasa masu tagomashi wa zaɓen dake tunkarowa domin neman samun kaiwa gaci.
An kuma fahimci cewar, za a karkaɗe tsohon jerin sunayen wakilan ƙasa (ambassadors) da za a naɗa zuwa ƙetare da tuni suke zaman jiran ba su muƙamai na sakayya, waɗanda kuma suke fushin rashin yi masu alfarma tun kafuwar gwamnati mai ci yau kimanin shekaru biyu kenan.
Sabon tsarin ya wajabta yin garanbawul wa majalisar gudanarwa (cabinet) ta gwamnatin Tinubu ta yadda za a shigo da sabbin jini cikin ta, husasan ma kututai ko jiga-jigan wasu mambobin CPC waɗanda suke zaune kara-zube daga ɓangaren tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta yadda za a yi masu shingen ƙetarawa gami-gambizar siyasa ta Atiku. Waɗanda za a ba su muƙaman kututan ‘yan siyasa ne da suke da tagomashi wajen sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a wa’adin mulki na biyu.
Domin kwantar da hankalin mambobin na CPC cikin gamayyar su da mambobin APC, an zayyana tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Almakura wanda wani jigo ne a ɓangaren CPC da zai maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa. Kasancewar Almakura shugaban jam’iyya, zai zama kadarko wa sulalewar mambobin CPC zuwa faɗawa cikin gamayyar ta Atiku, kamar yadda barazanar ke nunawa.
Majiyar ta bayyana cewar, za a kuma yawaita ɗauka masu wakilcin Nijeriya (ambassadors) zuwa ƙasashen ƙetare domin ɗinke ɓarakar tafiya tare cikin jam’iyyar ta APC.
Ta ƙara da cewar, “Za’a yi bibiyar jerin sunayen waɗanda aka zayyana domin naɗa su wakilancin ƙasa a ƙasashen waje saboda a ƙara yawan su, husasan za a ɗauko daga cikin mambobin CPC da aka fusatar na lokaci mai tsawo, har ma da wasu dakarun ‘yan jam’iyyar ta APC.
“Wasu ma daga cikin waɗanda aka zayyana sunayen nasu da aka yi hasashen za su wakilci ƙasa, za a ɗaga likkafarsu zuwa matsayin mambobin majalisar gudanarwa (cabinet) cikin canje-canjen baya-bayan nan da ake ƙoƙarin aiwatarwa,” a cewar majiyar.
Majiyar ta kuma bayyana cewar, wasu shugabannin na hukumomin gwamnatin ta Tinubu, waɗanda ake ganin ba su da karsashin farauto ƙuri’o’in zaɓe, za a ma saukar da su daga kan muƙamai ko kujerun da suke kai.
“Wasu ma shugabannin sassan gwamnati ta Tinubu (CEOs of MDAs) waɗanda sam ba su da muhimmancin ƙarawa miya zaƙi a zaɓen shekarar 2027 mai gabatowa, za a sauke su dungurumgum daga kan kujerunsu, koda suna da sauran lokuta na wa’adodin zamansu akan kujerun su,” a cewar majiyar.
“ɗaukar waɗannan matakai ya zame wajibi domin aiwatar da daidaito a tsakanin mambobin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar na kaucewa duk wani kwazazzabo da zai kawo ko haddasa tuntuɓe.”
Wannan kafa ta watsa labarai ta kuma gano cewar, wani shirgin na wannan tsarin, ana yin sa ne da zummar maƙalo jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa KwanKwaso zuwa komar APC, da kuma kwantar da rikicin masarautar Kano, ta yadda za a fifita Sarki na 16, Lamido Sanusi, wanda yake da goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, da yake da karsashin jawo hankulan kanawa su rumgumi sabon shirin shugaban ƙasa na farfaɗo da lamuran rayuwa (Renewed Hope Agenda).
A dai halin da ake ciki yanzu, daga can ƙololuwar tiƙewar siyasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wasu jiga-jigan masu basira da iya yakana na jam’iyyar APC umarni da su yi dukkan iyawarsu na maƙalo Injiniya Rabi’u Musa KwanKwaso cikin jam iyyarsu ta APC, gabanin tirka-tirkar shekara ta 2027 idan Mahukunci ya nuna mana.
Shi karan kansa Rabi’u Musa KwanKwaso an ba shi damar zayyana sunayen waɗanda yake so su kasance ministoci, shugabannin sassa da hukumomin gwamnatin tarayya, har ma da waɗanda za su kasance wakilan Nijeriya ko jakadu zuwa ƙasashen ƙetare, kamar yadda aka ba shi waɗannan garaɓasoshi. A fakaice dai, ana hasashen KwanKwaso zai maye kujerar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a zaɓuɓɓukan fitar da gwanaye ‘yan takarkarun tsayawar zaɓuɓɓukan kujerun mulki dake tafe, domin ya ƙarawa zaɓen Tinubu tagomashi, yadda za a murƙushe barazanar guguwar gamin-gambizar Atiku da CPC, wacce Buhari yake goyawa baya.
“Haka-zalika, tirka-tirkar masarautar Kano dake murƙusuwa tana samun warwara, kamar yadda ake shirin Lamido Sanusi shi da ke da nasara, yayin da ake shawartar Aminu Ado Bayero ya rumgumi ƙaddarar haƙuri, tare da janye dukkanin ƙararrakin da ya shigar daga kotuna. Za a rarrashe shi da niyyar ya kasance wakilin Nijeriya a cikin ɗaya daga ƙasashen Larabawa, walau (ƙatar, Kuwait ko Saudiyya),” kamar yadda majiyar ta ruwaito.
Haka nan kuma, wata majiya da ba a tantance ba, tana mai ruwaito da cewar, waccar guguwar ta gamin-gambiza ana da’awar ta yi tarurruka da wasu hafsoshin sojoji masu ritaya ‘yan asalin arewacin ƙasar nan, waɗanda ake da yaƙinin za su iya takawa jagorancin Tinubu birki.
Haka ma, wata majiya da ake yin ƙaulani ta ruwaito cewar, wasu dakarun tsofaffin shugabannin sojojin ƙasar nan (OBJ, IBB, TY, AAA da Gusai) sun yi zaman shawarwari a ranar 12 ga watan Afrilu, 2025, inda suka tattauna kan batutuwan tattalin arziki, walwala da siyasar ƙasar nan.
“An dai ruwaito cewar, makamantan dakarun siyasa irinsu Atiku Abubakar da wasu masu hazaƙar faɗi a tirka-tirkar 2027 sun halarci wancan taron. Duk da cewar, taro ne na sirri, wasu majiya sun habarto cewa, an ɗauki ƙwararan matakai na fito da wani gangarama da za su buga da Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar ta 2027, da zummar haɗa kan al’ummar ƙasar nan, na uwa ɗaya, uba ɗaya, da kuma domin ɗorewar dimokradɗiyya a Nijeriya.
