Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
Ƙungiyar cigaban al’ummar Jasawa (JCDA), ta bayyana cewa gobarar da ta tashi da tsakar daren Talata a babbar kasuwar Jos ta bar al’ummarsu cikin baƙin ciki da ɗimuwa.
Ƙungiyar ta JCDA ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban sakataren ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Muhammad Tanko Shittu ya sanyawa hannu, inda ta jajentawa waɗanda abin ya shafa.
Sanarwar ta buƙaci gwamnatin Jihar Filato da ma’aikatar harkokin jin ƙai ta tarayya da su basu tallafin gaggawa ta fuskar jari da kayan agaji ga waɗanda suka yi asara.
“Gobarar da ta faru a babbar kasuwar Jos, inda rahotanni suka nuna cewa ɗaruruwan shaguna da kadarori da kuɗinsu ya kai Naira biliyan ɗaya suka ƙone, ta bar al’ummarmu cikin damuwa da baƙin ciki. Muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga iyalai, abokai da masu shagunan da suka yi asarar dukiyoyinsu da hanyoyin samun abin dogaro a wannan mummunan lamari.”
“Wannan al’amari mai tayar da hankali ya sake nuna yadda kasuwanninmu ke cikin haɗari idan gobara ta tashi, tare da buƙatar ɗaukar matakan tsaro da taimako cikin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa,” in ji JCDA.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta gudanar da bincike sosai, da kuma samar da motocin kashe gobara a cikin kasuwar domin samun damar kai ɗauki cikin lokaci idan wani abu ya faru.
“Haka kuma muna kira ga hukumar samar da agajin gaggawa ta Jihar Filato (PLASEMA) da ta samar da taimakon gaggawa da agaji ga waɗanda lamarin ya shafa, ta hanyar amfani da ƙwarewarsu a fannin kulawa da bala’o’i.
“Muna kuma kira ga ma’aikatar harkokin jin ƙai ta tarayya da ta bayar da taimakon jin ƙai, ciki har da tallafin kuɗi ga waɗanda abin ya shafa,” in ji sanarwar JCDA.
