Najeriya ba za ta sallama wa ‘yan bindinga ba – Tinubu

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana wa sojoji dake yaƙi da ‘yan bindinga a Katsina cewa gwamnatin Najeriya ba za ta bar wani yanki na jihar a hannun ‘yan ta’adda ba.

A cewar shugaban ƙasar ƙaryar ‘yan bindinga da masu taimaka masu ya ƙare a ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin samar wa sojojin Najeriya kayan aiki domin fatattakar ayyukan ‘yan bindiga a Arewacin ƙasar.

Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma’a a wata ziyara da ya kai Jihar Katsina, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ɓarayin daji, shugaban ƙasar ya ce matsalar ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ɓarayin daji ta jima a ƙasar.

“Ƴan Najeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Najeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare”, in ji Shugaba Tinubu.

”Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗa da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙarfin da za ku iya murƙushe duk wata barazana a ko’ina ta ɓulla”.

A nasa jawabin gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki shekaru biyu da suka gabata gwamnatinsa ta mayar da hankali kan inganta noma, samar da kayan more rayuwa, samar da aiyuka da kuma samar da tsaro.

Gwamnan ya kuma yi bayani game da yadda gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar samar da takin zamani ga manoma da kuma kayan noma na zamani.

Radda ya kuma sanar da al’ummar jihar irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi don samar da kayan more rayuwa ciki harda sabunta taswirar jiha gami da samar da ruwan sha.

Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya yabawa gwamna Raɗɗa bisa salon jagorancinsa a jihar ta Katsina inda ya kira shi da “mai gaskiya da nuna ƙwazo”.

By ukarofi