
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC, ta kama daraktoci da manyan jami’an da aka tsige a kwanan nan na kamfanonin matatun Fatakwal da Warri da kuma Kaduna.
An yi hakan ne bisa zargin su da hannu s laifin sauya aƙalar wasu kuɗaɗe da aka ware domin gyaran matatun, waɗanda adadinsu ya kai Dala biliyan 2.9.
Jaridar ‘Newspoint Nigeria’ ta ruwaito cewa, bincike ya nuna yadda EFCC ta ke binciken yadda aka sarrafa $1,559,239,084.36 da aka bai wa matatar Fatakwal da $740,669,600 da aka ware wa na Kaduna da kuma $656,963,938 ga na Warri.
Wata majiya daga Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL, ta ce an gano Naira biliyan 80 acikin asusun ɗaya daga cikin daraktocin da aka kama.
Haka kuma masu gudanarwa da ƙwararru sun soki NNPCL bisa yaudarar al’umma da cewa matatun sun fara aiki haiƙan musamman na Fatakwal da Warri tun bayan dawowarsu aiki a watannin Nuwamba da Disamba, 2024.
EFCC ta zayyano waɗanda ake tuhuma da hannu a badaƙalar da suka haɗa da Abubakar Yar’Adua, Mele Kyari, Isiaka Abdulrazak, Umar Ajiya, Dikko Ahmed, Ibrahim Onoja, Ademoye Jelili, da Mustapha Sugungun.
Sauran sun haɗa da Kayode Adetokunbo, Efiok Akpan, Babatunde Bakare, Jimoh Olasunkanmi, Bello Kankaya da kuma Desmond Inyama.
